TAKADDAMA

TAKADDAMA DA HANYOYIN SASANTAWA FITOWA NA 2: CANJE CANJEN TAKADDAMA

Yawancin mutane idan suka ji wannan kalma “Takaddama ko Hargitsi” abin da ke shiga zuciyarsu shine yaki, ko fada, ko mahawara, ko yamutsi, ko damuwa, ko farmaki da sauransu.

Mukan dauki takddama kamar wani abu ne dab a shi da kyau wanda ya kamata a guje shi ko a kauda kai daga gare shi ko ma a yake shi.

Shin kowane lokaci ne takaddama ked a mummunan tasiri ko sakamako? Mutanen “Sin” wato (China) bas u yin irin wannan tunanin. A harshensu “takaddama” tana nufin samun dammar kawo sauyi, ko sayar da rai ko hadari.

Abin nufi a nan shi ne Kalmar takaddama, ba lallai ne ta kasance abu mai kyau ko maras kyau ba. Sakamakon takaddama ya dangata ne ga yadda muka tunkare ta. Irin tarbiyya da horon da muka samu daga iyayenmu tun muna kanana, da halaye da dabi’unmu da yanayin yadda muke fahimtar abubuwar da yanayin wuraren da muka taso suna daga cikin abubuwan da ked a tasiri wajen yadda muke tunkarar takaddama.

Mutanen da suka dauki takaddama a matsayin abu maras kyau, sukan fuskace ta a karkace don haka sakamakonta ma yakan zo musu da muni. Amma daukar takaddama a matsayin abu mai amfani yana taimaka wa mutun ya shawo kanta kuma har sakamakonta ya yi masa amfani. Misali takaddama takan taimaka a zauna a tattauna matsaloli, a fahimci juna har a kulla kyakkyawar dangantaka a tsakanin alumma. Yin hakan kuma yakan kara kaunar juna a zukatan jama’a su yi zaman lafiya kuma su sami ci gaba. Idan aka sami hanyar ko dammar yin musayar ra’ayi ko yanayin rayuwan jama’a zai canja ta yadda kowa zai rika girmama kowa.

Dole ne a rika samun afkuwar takaddama a tsakanin al’umma a kai a kai saboda bambance bambance da ke tsakaninmu.

Saboda haka wajibi ne mu inganta fahimtar mu game da takaddama da kuma bukatar mu fahimci cewa takaddama tana iya zama wata dam ace ta kawo canji da cigaba idan aka sarrafa tad a kyau, maimakon a bar tat a yi sanadin barkewar mummunan rikici.

Ba kowane lokaci ba ne muke haddasa takaddama da muka samu kanmu ciki, amma a kowane lokaci muna da ikon zaben irin hanyar da muke so mu tunkare ta har mu shawo kanta.

Sai kuma Idan Allah ya Kaimu Ranar Juma’a mai zuwa (29/04/2016) za mu shigaba

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments