Ilimin-Komfuta

360 Security: Ingantarciyar Kariya Ga Wayar Andriod

Assalamu alaikum. Barka mu da warhaka. Allah (SWT) Ya sake kawo mu wani makon inda za mu Kara kawo muku shirin Ilimin Kwanfuta.

Makonin baya shirin ya kawo muku Muhimman App na Tsaro Guda Biyar ta Kwamfutar Hannu ko Wayyar Hannu mai tsarin Andriod, a inda muka jero muku applications guda biyar wa’inda za ku iya amfani da su wajen kare wayyoyin ku.

Daga cikin wa’innan applications din, muka nuna a ra’ayin mu 360 Security ne Ya ke kan gaba wajen kariyar.

A wannan shirin za mu nuna muku yarda ake amfanin da wannan fittarciyar Application din.

YARDA AKE SANYA SHI A WAYA

360 mobile security ana samin shi ne a Google Play Store cikin jerin dubanin applications, kuma a kyauta ake sanya shi. Za a iya sami shi idan aka latsa => 360 Security

YARDA AKE AMFANI SHI
Idan aka latsa shi daga jerin applications da aka riga aka sanya a wayar,
360-security-on-phone-menu
Zai bude shafin farkon da mai wayar zai fara gani shine kamar wannan hotor.
360-security-boot
Bayan yan sakoni kadan, sai ya bude babar shafin 360 Security. A wannan babban shafin ne mai wayar zai ga bangare daban daban wa’inda suka hada da:

BOOST:

Sashe mai kara caja kwakwalway wayar wajen aiki da sauri, Za a latsa alamar mita dake rawun ne inda aka rubuta Boost don ya fara aiki. Cikin sakan biyar ko kasa da haka zai gama aikin shi kuma ya bayyana rahoton nasarar da yayi wurin caja wayar.

360-security-boost

CLEAN

Sashe mai sabtace kwakwalwar wayar daga duk fayil mara amfani. Shi ma idan aka latsa Scan, zai bincika kwakwalwar wayar don neman fayiloli da suka kirkiri kasu (wanda ake fi sani da Junk) do share su, inda zai kara samin sarari a kwakwalwar wayar.

360-security-clean

ANTIVIRUS

Sashe mai bincikar wayar da dubiya da magance duk wani cutar virus. shi kuma wannan bangaren yana kulawa ne da kuma magance duk wani virus da ya shiga cikin wayar, inda duk lokacin da aka latsa Scan, zai zagaye duk fayilolin da apps da suke cikin wayar don neman virus. Idan ya sami virus, zai sanar da hakan kuma ya bada inda za’a latsa don magace su.

360-security-antivirus

 

A kowani lokaci da ya gama duk aikin da aka sa shi, ya kan kara bayyanai akan wasu matsolin da wayar yake fama dashi (idan akwai), kamar irinsu, nuna apps da suke taimakawa wajen kashe battery, zafin waya (temperature) da saura su. Kuma ya nuna alamar inda za’a dana don mangance matsalar.

360-security-more-issues

Kuma a bangaren MENU din shi,

360-security-menu1

za’a sami wasu aiyukan da 360 Security ke yi kamar su:

360-security-apps-on-menu

  1. Data Monitor: mai kula da data da mai waya ke amfani da shi, wurin nuna me adadin datar dayayi amfani da shi
  2. Call & SMS Filter: Don tantance masu kira da turo sakoni.
  3. Find my Phone: Don kunna naurar da za’a iya daukar hoto kuma ya nuna inda wayar take idan aka sace wayar.
  4. App Lock: Don kulle apps da mai waya bai so ana shiga sai ansa kalmar sirri
  5. da sauran su

Yana da kyau a shiga a lallatsa wa’inan na’urorin ko da sau daya a mako. Amma a kullun, mai wayar ya dinga caja wayan ta hayar boosting dinshi da alamar 360 security da ya makale a sashin gabar wayar (Home Screen)

360-security-icon-phone-home

Wannan alamar, a duk yayin da launin shi ya tashi daga shude ya ko ma ja, to yana bukatar a latsa shi don cajin (ta bangaren aiki) wayar. Idan mai waya ya latsa shi zai ga menu kamar haka

360-security-phone-home-options

Inda zai ga alamar rawun da ke saman shi. Kana dana shi bayan ‘yan sakoni kadan zai bada rahoton aikin da ya yi.

360-security-phone-home-boost-result

Ana za mu tsaya, sai idan Allah (SWT) Ya kai mu mako mai zuwa idan zamu kawo muku wani sabon shirin.

Mu ji ra’ayin ku, ko karin bayani, ko kuma tambaya akan wani bukartar sanin ku ta bangaren Ilimin kwamfuta.

A huta lafiya.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website