Daga Malamanmu – Girman kai 3

Daga Malamanmu 3

Assalamu alaikum ‘yan’uwa, barkarmu da saduwa a wannan shiri namu na Daga Malamanmu, a kuma wannan gida Fitila24, dan cigaba da kawo-muku wannan shirin Daga Malamanmu, inda muke kawo muke karatu a cikin littafin Malaminmu Ash-sheik Abdulwahhāb Abdullah.

Wannan shie shiri na 3….

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

TAMBAYA TA 3:
Shin yin TSAFTA da yin ADO yana cikin girman kai?

AMSA
Yin tsafta da yin ado da saka tufafi ma su kyau ba ya cikin girman kai. Barima musulunci ya kwadaitar da yin tsabta ta gangar jiki da ta tufafi da muhalli kamar yadda ya zo a fadar Allah (swt) Suratul Muddassir aya ta 4.

Wasu daga cikin malaman tafsiri sun fassara ta da cewa: “kuma ka tsarkake tufafinka”.

Haka kuma ya tabbata cewa manzon Allah (saw) ya fi kowa tsafta, ya kasance mai yawan yin asuwaki, kuma ya umarci al’ummarSa da yin aswaki da tsabtar gangar jiki da yanke farce da cire gashin hammata da na mara da rage gashin baki da yin shayi (kaciya) da sauransu. Kuma ya umarci alummarSa da yin wanka da sanya tufafi ma su kyau da sanya turare. Ya kuma kasance yana hani ga warin jiki da warin baki da abin da ya ke jawo su; kamar cin Tafarnuwa da danyar Albasa, da rashin yin askin hammata da duk abin da zai janyo doyi a jiki, musamman a lokacin da mutum zai hadu da ‘yan uwansa musulmi, a masallaci ko taron jama’ah da sauransu.

Hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (saw) ya ce: “Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (saw) – kuma shi wannan mutumin ya kasance kyakkyawa ne, sai ya ce: An sanya mini son kyau, kuma an ba ni kyau kamar yadda kake gani, har ba na son wani ya dara ni ko da da kyawun hancin takalmi. Shin wannan girman kai ne? Sai Manzon Allah (saw) ya ce: A a, (Ba shi ne girman kai ba); girman kai shi ne qin karbar gaskiya da wulaqanta mutane.” – ( – Hadisi ne ingantacce: Adabul Mufrad, tahakikin Muhammad Iliyas Al-Barah hadisi na 1556, shafi na 444, bugun Daru Ibn Kasir. Abu Dauwd Shi ma ya ruwaito shi a cikin Kitabul Libas, hadisi na 3569. As-Shaikh Muhammad Nasiruddinil Albaniy ya inganta shi a cikin silsilatul Ahadisis sahihah, (4/168).

Wannan ya nuna cewa son tsafta da kwalliya da makamantansu ba su ne girman kai ba.

Sai mun hadu a fito ta 04 da yardar Allah

Wallafar:- Shaikh Abdulwahhāb Abdullah

Gabatarwa:- H.Y Kakuri (Abu~Sajida)

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website