Daga malamanmu – Girman kai 4

Daga Malamanmu 4

Assalamu alaikum ‘yan’uwa, barkarmu da saduwa a wannan shiri namu na Daga Malamanmu, a kuma wannan gida Fitila24, dan cigaba da kawo-muku wannan shirin Daga Malamanmu, inda muke kawo muke karatu a cikin littafin Malaminmu Ash-sheik Abdulwahhāb Abdullah.

GIRMAN KAI SABABINSA DA HADARINSA DA KUMA MAGANINSA.

TAMBAYA TA 4:
Mene ne sababin da yake sanya mutum girman kai, ko jiji da kai?

AMSA:
Sabubban da su ke kawo girman kai da ji-ji-da-kai su na da yawa, amma ga mafiya shahara daga cikin su:

1. Alfahari da asali
2. Yawan dukiya
3. Ilimi
4. Mulki ko sarauta
5. Qarfi
6. Yawan mabiya
7. Fasahar harshe
8. Yawan ibada
9. Kyawun halitta.

Ga bayananasu kamar haka:

1- Asali: Yakan sanya mutum yin girman kai, imma asalin jinsi ko na iyaye ko na qabila.
Asali jinsi: Dalilin mu na cewa asalin jinsi ya kan sanya mutum yin girman kai shi ne: Abin da ya faru tsakanin Iblis da Annabi Adam (as) yayin da Allah (swt) ya umarce shi da ya yi wa Annabi Adam sujjada sai ya qi. Allah (swt) ya ce: “Sai Allah ya ce, mene ne ya hanaka yin sujjada ga abin da na halicce shi da hannu na? shin girman kai ka yi? Ko ka kasance a cikin ma su dagawa (ne)? Sai ya ce: Ni na fi shi (yana nufin ya fi Annabi Adam), ka halicce ni ne daga harshen wuta, shi kuma ka halicce shi ne daga tabo.” (Suratu Sad, aya ta 75 – 76).

A nan Iblis ya yi girman kai ne don asalin halittarsa; yana ganin cewa asalin da aka halicce shi da shi wato harshen wuta ya fi abin da aka halicci Annabi Adam da shi, wato tabo. Wannan kuwa zatonsa ne da jahilci don ba shi da wani dalili cewa harshen wuta ya fi tabo. Barima, Allah ya fifita Annabi Adam (as) akan sa don haka ya umarce shi da ya yi ma sa sujjada shi da malaiku wadanda su ke daga cikin fiyayyun halittun Allah.

b)Yin alfahari da iyaye:
Wannan dabia ce ta mutanen jahiliyya kafin zuwan musulunci, don haka manzon Allah (saw) ya hana alummarSa wannan mummunar dabiar, kamar yadda hadisi ya tabbata daga Abu Malik Al-Ashariy (ra) ya ce: Haqiqa Manzon Allah (saw) ya ce:
“Halaye guda hudu da su ke cikin al’ummata su na daga al’amuran jahiliyyah, ba za su dena su ba, yin alfahari da nasaba (iyaye da kakanni) da sukar nasabar wani/wasu da danganta samun ruwan sama ga taurari da daga murya ya yin kukan kera.” (Sahihu Musulim, hadisi mai lamba 934 shafi na 933, bugun Baitul Afkar addanliyyah).

Kuma hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce:
“Haqiqa Allah madaukakin sarki ya tafiyar mu ku da girman kai da ji-ji-da-kai na jahiliyya, da alfahari da iyaye. Mumini mai tsoron Allah ko kuma fajiri tababbe mara rabo, dukannin ku banu Adam ne, Annabi Adam kuma daga qasa ne. Lallai ne wadansu mazaje su daina alfahari da wadansu mutane (iyayensu da kakaninsu) wadanda su ke su gawayi ne daga gawayin jahannama ko lallai su sun kasance mafi wulaqanta a gurin Allah fiye da buzuzu wanda yake tura qazanta da hancinsa.” (Sunan Abi Dawud, hadisi mai lamba ta 5116, shafi na 551 bugun Baitul Afkarid Dauliyyah).

A nan za a gane cewa jahilci shi ke sa wa ake alfahari da iyaye da sukar nasabar wasu. Shi ya sa Manzon Allah (saw) ya danganta su da jahiliyyah. Don haka idan ka ga mutum yana alfahari da iyaye da sukar nasabar wani/wasu ka tabbata jahili ne koda ya yi karatu.

c)Asalin Qabila:
Mutum ya kan yi girman kai don qabilarsa, ko wani launin halittarsa. Wannan yana daga cikin munanna dabiu na jahiliyya wanda manzon Allah (saw) ya hana, domin hadisi ya tabbata daga Maarur Bin Suwaid ya ce:
Mun wuce Abu Zarr (ra) a wurin da ake kira Rabzah, sun yafa mayafi iri daya shi da bawansa. Sai mu ka ce: Ya Aba Zarrin da ka haxda guda biyun da ya zamanto ma ka cikakken ado (kamar dai riga da wando) sai ya ce: (dalilin da ya sa haka shi ne) mun yi ce-ce ku-ce da wani mutum daga yan uwana, kuma mahaifiyarsa ta kasance ba’ajamiya ce (ba’ajamiya wato wacce ba balarabiya ba, dadin dadawa kuma bakar fata) Sai na aibata shi da mahaifiyarsa, sai ya kai qara ta wajen manzon Allah (saw), sai na hadu da manzon Allah (saw), sai ya ce: kai Abu Zarrin! Haqiqa kana da dabia ta jahiliyyah, sai na ce: ya manzon Allah (saw), duk wanda ya zagi mutane za su zagi babansa, da babarsa. Sai ya ce: ya Aba Zarrin! Haqiqa kana da dabia irin ta jahiliyyah. Su yan uwanku ne, Allah ya sanya su a qarqashin ku, ku ciyar da su daga abin da ku ka ci ku tufatar da su daga abin da ku ka tufatar da kanku, kuma kar ku dora musu aikin da ya fi qarfin su, idan kuwa kuka xdora mu su aikin sai ku taimake su. (Bukhari da Muslim ne suka rawaito, kuma wannan lafazin riwayar Muslim ne. Duba Sahihul Bukhari hadisi na 30 da na 2545, da na 6050, bugun Baitul Afkar Ad-Dauliyyah. Da Muslim hadisi na 1661, shafi na 684, bugun Baitul Afkar Ad-Dauliyyah).

A nan manzon Allah (saw) ya nuna fushinSa da damuwarSa akan abin da Abu Zarrin (ra) ya aikata, duk da irin qaunar da yake yi ma sa, sai da ya mayar ma sa da martani ya ce: lallai kana da dabia irin ta jahiliyya. Don mene ne za ka aibata dan uwanka domin mahaifiyarsa baqa ce? Daga nan Abu Zarrin (ra) bai qara aibata kowa ba. Barima, idan ya tufatar da kansa kuma sai ya tufatar da bawansa irin wadannan tufafin. Allah shi ne masani.

Mun hadu a fito ta 05 da yardar Allah

Wallafar:- Shaikh Abdulwahhāb Abdullah

Tare da ne:- H.Y Kakuri (Abu~Sajida)

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website