Gidan Aure – 5

Assalamu alaikum, ‘yan’uwa ma’abota bibiyar wannan gida namu Fitila24 a kuma wannan shiri namu na Gidan Aure

Da yardar Allah zamu cigaba daga shawarwarin da nake bawa ‘yan’uwana mata dan inganata Gidajan Auranmu, zamu fati zuwa ga shawara ta biyar….

5 KIYIWA MIJIN KI MURMUSHI

Murmushi alama ce ta sabawa, ki sanya shi akan leban ki domin mijin ki ya gani duk lokachin da ya kalleki

Manzaon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: “Kar ku raina ko wani irin aikin alkhairi, ko da ka hadu ne da dan uwan ka da sakakkiyar fuska”

An tambayi wani MIJI:
Menene abinda yafi faranta maka a gun matar ka
Sai yace:
Fuskar ta mai walwala da dariya, nishadin ta, tare da cikakken farin cikin ta

Dayan kuma yace: Dukkan gajiya ta tana tafiya yayin da mata ta ta fuskance ni ta na mai dariya

Na ukun yace: Murmushin mace ga mijin ta rabin farin ciki ne, daya rabin kuma yana daga yalwal da take gidan ka

Wani talakan Mabarauchi ya rayu da matar sa a cikin farin ciki da jindadi, yana kuma daga al’adar matar sa tana yiwa mijin ta ban kwana a safiya yayin da zai tafi aikin sa, tana mai murmushi kuma ta tare shi da yamma tana mai murmushi, ya kasance kuma yana son wanna abun, shi yasa ma ya nema daga gare ta ta cigaba da wanna halin na ta a duk sanda ya gan ta

Yayin da mijin ta ya mutu sai ta daukarwa Allah alkawari ba za ta kara yiwa wani murmushi bayan mijin ta

Ta rayu tsahon rayuwar ta tana mai azumin murmushi

Ya yar uwa ta musulma shin ke wa kike yiwa murmushi
Mijin ki
Ko kuma ko wani shashasha, soko

Mu hadu a shawara ta shida insha Allah

Gabatarwa:- Umar Ya’akub
Tare dani:- Maman Mufeeda (Auti Halimat).


 

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website