Gidan Aure – Kinemi yardar mijinki -6

Assalamu alaikum, ‘yan’uwa ma’abota bibiyar wannan gida namu Fitila24 a kuma wannan shiri namu na Gidan Aure

Da yardar Allah zamu cigaba daga shawarwarin da nake bawa ‘yan’uwana mata dan inganata Gidajan Auranmu, zamu fati zuwa ga shawara ta shida….
6- KI NEMI YARDAR MIJIN KI

Yardar mijin ki itace mabudin farin cikin ki, kiyi kokari ki rabauta da yardar sa, saboda shine hanyar ki zuwa gidan aljanna.

Manzan Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: Duk matar da mijin ta ya mutu yana mai yarda da ita zata shiga aljanna

Annabi Dawood yana cewa: mace ta gari hular sarki ce wadda aka yi mata ado da zinare, duk lokachin da mijin ta ya gan ta tana sanyaya masa idanuwan sa

Sata mata ta ga mijin ta a cikin mafarki bayan rasuwar sa, yana zaune a kofar wani daki wanda yake a kulle daga cikin dakunan aljanna,
Sai ta tambaye shi na waye wanna
Sai yace: wanna dakin na ki ne, babu wata da ta taba shiga cikin sa, saboda na mutu ina mai yarda dake

Wata mata ma’abociyar addini da halaye na gari ta auri wani mai kudi dan kasuwa
Ta kasance tana himmatuwa wajan yi masa hidima kuma tana kin yin barchi saboda mijin ta
Sai yayi rashin lafiya wata rana
Sai ta zauna a wajan sa ta sunbatar hannusa da kafar sa tana kuka saboda ciwon dake damun sa

Sai aka ce da ita: me isa kike aikata wadanna abubuwan
Ki saukakawa kan ki mana
Za ki iya halakar da kan ki

Sai tace: ina aikata haka saboda yardar miji na tana bakin kofa cikin kofofin aljanna, bana so a haramta min shiga

Ya yar’uwa ta musulma, anya kuwa kina yiwa mijin ki hidima da aikace aikace
Shine yake fara yin barchi ko kece
Anya kina damuwa da damur sa

Inajin dai yan aikin gida ne suke kula miki da miji
Sune suke masa girki
Su share masa dakin barchin sa
Su wanke masa kayan barchin sa
Su kawo mai ruwan da zai sha
Su dauko masa jakar sa idan ya dawo daga aiki

Anya kuwa kina son ki shiga ALJANNA

Mu hadu a shawara ta bakwai cikin yardar Allah

Gabatarwa:- Umar Ya’akub
Tare dani:- Maman Mufeeda (Aunty Halimat).

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website