Hausa da Hausawa – Episode 10 – YAQE-YAQE A QASAR HAUSA

muhimman yaqe-yaqe a qasa Hausa bayan tafiyar Annabi Isah (A.S) har zuwa qarshen qarni na 18.

Haka kuma sun yi yaqe-yaqe domin su qwace gari, bayan wani lokaci sai aka ci gaba da yaqe-yaqen tsakanin garuruwa, amma ba domin samun gari ba sai domin ganima.

Mahdi (1978) ya bayyana yaqe-yaqen wajen qasar Hausa ne suka qarfafa yaqe-yaqe cikin qasar Hausa domin babu wata qasar da za ta zuba ido a yayin da abokiyar karawar ta ke fadada mulkinta ta hanyar samun sababbin yankunan mulki.

A karni 13 Katsina ta yaqi Kwararafa a qarqashin mulkin Qorau, a karni na 14 Kano a qarqashin mulkin Yaji ta yaqi Warji wanda shi ne Ningi a yanzu.

Zamfara da Kebbi su ma sun yi yaqe-yaqe inda Zamfara ta yaqi maqwabtan ta na kudu zuwa yankin Yawuri, ita kuma Kebbi suka mamaye Nufe.

Ita kuma qasar Zazzau a wancan lokacin ba zato ba tsammani ta kusan mamaye dukkan qasar Hausa da kuma qasashen Bauci. Wanda ‘yar sarki wato, Amina ta shugabanci wannan cin qasashen.

Haka dai abin ya dinga faruwa har zuwa qarni 19, kodayake a wannan lokacin hamayyar neman mulki tsakanin qasashen Hausa ta qare kuma jihadin Dan Fodiyo ne ya gyara barnar da suka yi wa juna.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website