Hausa da Hausawa – Episode 7 – YANAYIN QASAR HAUSA

Qasar Hausa qasa ce wadda take galibinta shimfidaddiya ce, kuma tana da yawan sarari, akwai tsaunuka da tuddai jifa-jifa. Kuma manyan koguna biyu sun ratsa ta cikin ta, kogunan su ne; kogin Rima da kogin Hadejiya, kogin Kwara shi ko ya zama kamar iyaka daga yammacin qasar.

Idan aka dubu kogunan za a ga cewa, kogin Rima ya taso daga qasar Zamfara ya gangara arewa zuwa Nijar. Sannan ya karkata kudu ya bi ta yamma da Sakkwato ya je fada cikin kogin Kwara. Kogin hadejiya kuwa ya faro daga qasar Kano, daga nan ya gangaro ya bi Gashuwa da Gaidam ya je ya shiga tafkin Chadi.

Akwai lokacin damina akan sami ruwa tsakanin watan mayu zuwa satumba, kuma ruwan yakan biya buqata wajen tafiyar da aikin gona. Lokacin rani yana farawa ne daga watan oktoba zuwa Afrilu. Lokutan su  ne , lokacin dari, wato hunturu da kuma lokacin zafi wato bazaar.

Qasar Hausa qasa ce wadda take albarkar noma domin fadama ce, dausayi saboda haka Hausawa suka sami damar kafa bukkoki da gidaje don kyautata sha’aninsu na noma.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website