Hausa da Hausawa – Episode 8 – DAZUZZUKAN QASAR HAUSA

Daji wuri ne wanda yake  ya yi nesa da gida, kuma babu komai sai tsirrai da itatuwa da namun daji da sauran halittun ubangiji madaukakin Sarki, idan ma za a samu jama’a to qalilan za a samu kurum , saboda haka dangane da dazuzzuka a qasar Hausa akwai iri biyu:

Na farko shi  ne DAJIN SAHEL wannan dajin yana daga arewacin qasar Hausa, yana da qaramcin itatuwa, wato itatuwa jifa-jifa ake samunsu, kuma gajeru ne. itatuwan da suke a wannan wuri sukan kade kanqat da rani. Idan kuma damina ta kusa sai su fara ganye. Ciyawa kuma dabbobi kan cinye rabinta, kuma su tattake rabi. Amma idan aka ruwan sama na farko da damina duk sai su tsiuro ko’ina.

Daji na biyu na qasar Hausa shi  ne DAJIN SABANNA wannan dajin yana daga kudu , a nan wurin itatuwa suna da tsawo kuma suna da kusanci da junansu. Ciyawa a nan kuma mai tsawo ce fiye da SAHEL, kuma wasu daga cikin ganyaye da ciyayi da ake samu a wannan wuri sukan shekara ba tare da sun bushe ko kuma kadewa ba.

A cikin qasar Hausa akwai ‘yan duwatsu jefi-jefi, akwai koguna manya da qanana da suka ratsa qasar, wasu suna kai ruwansu kogin kwara, wadansu kuma cikin Chadi.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website