Janaba

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
23/03/1438-HJRY
23/12/2016-MLDY

TOPIC= [HUKUNCE HUKUNCEN JANABA]

***** MUQADDIMA *****
Ina muku wasiyya da ni mai magana muji tsoron ALLAH SW, shi dayane da bashida kishiya! Shugabane da babu mai ja dashi! Mawadacine da bashida bukata! Mai karfine da babu abinda ke gagararsa a sama ko kasa! babu mai maida hukuncinsa da kaddararsa!

Na kasa khudubata gida 5, ga sunan daki daki=

{{1}} KALMAR JANABA A QUR’ANI DA HADISI:
Hakika Kalmar JANABA tazo a wasu wurare acikin ALQUR’ANI da HADISAN ANNABI SAW, Ga kadan daga ciki=
= ALLAH yace- “in kun kasance kunada JANABA to ku tsarkaka” (SRT MA’IDAH-6)
= ALLAH yace- “koda mai JANABA saidai mai tsallake hanya” (SRT NISA’I-43)
= MAIMUNA R/A- Matar ANNABI SAW tayi wanka a baho sai ANNABI SAW yazo zaiyi wanka da ragowar ruwanta- Sai tace- inada JANABA, Sai ANNABI SAW yace- “shi ruwan baya JANABA” <AS’HABUSSUNAN>

{{2}} MA’ANAR KALMAR JANABA- DA KUMA YADDA YAKE SAMUN MUTUM:
Shi JANABA shine wani abune da yake samun mutum ta daya daga hanyoyi 2=

1- fitan maniyyi don jin dadi a barci ko a farke sai ace da mai shi JANABA ta kamashi,
HUJJA- UMMU SULAIM tacewa ANNABI SAW- shin akwai wankane akan mace in tayi mafarkin saduwa?
Sai ANNABI SAW yace- E, in taga ruwa -maniyyi- <BHR & MSLM>

2- Kusantar mace (jima’i) koda basuyi release ba, wato koda maniyyi bai fitobaba,
HUJJA- ANNABI SAW yace- “idan yazauna atsakanin gabobinta guda 4- wato kafafu 2 da hannaye 2- yayi jima’i da ita to wanka ya wajaba koda baiyi release ba” <BHR & MSLM>

{{3}} HUKUNCIN JANABA:
Hukuncin wanda JANABA takamashi shine- WANKA,
= ALLAH yace- “in kunada JANABA kuyi tsarki” [SRT MA’IDA-6]
=Ya fassara wannan tsarkin da wanka a [SRT NISA’I-43]yace- mai JANABA kada yakusanci salla sai yayi wanka
= ANNABI SAW “idan yazauna tsakani gabobinta 4 yayi jima’i da ita to yayi wanka”
Fitan maziyyi ko wadiyyi ba’a daukansu JANABA, hukuncinsu tsarkine irinna bawali,

{{4}} SIFFAR WANKAR JANABA NA KAMALA:
UMMUL MUMINEEN AISHA R/A ta kawo siffar wankar ANNABI SAW daga JANABA tajero abubuwa 7 kamar haka ajere=
1- “yana wanke hannunsa sau 3”
In daga barci ka farka wanke hannun wajubine amma in ba daga barciba sunnane
2- “sai yawanke farjinsa da hagunsa”
3- “sai yayi alwala”
4- “sai yajika yatsunsa da ruwa yashigar dasu tsakanin gashin kansa yana mutsutstsuka kansa”
Yin hakan riga kafine daga ciwon kai, domin yayinda maniyyi ke fitowa kafofin gashin kai yana buduwa, in anzo wanka aka watsa ruwa ba tareda mutsutsukewarba yana taruwa a murfin kai yasabautarda ciwon kai,
5- “sai yazuba ruwa akansa sau 3”
6- “sai yazuba ruwa a sauran jikinsa”
Mustahabbine afara da tsagin jiki na dama kafin na hagu,
7- “sai yawanke lafafunsa” <BHR & MSLM>
A wata ruwaya- tace- sai nazo masa da tawul don yatsame ruwan jikinsa sai yamayar bai karbaba sai yana tsantsame ruwan da hannunsa,
= IMAMUL ALBANY yace- bayan kayi wankar JANABA in kaso katsantsame ruwan jikinka da tawul in kuma kaso kabari, domin shi ANNABI SAW in ana sanyi yana tsantsamewa in kuma ana zafi sai yabari don bukatar sanyayawa, <ALHAAWY MIN FATAWAL ALBANT>

{{5}} WASU HAKUNCE-HUKUNCE MASU ALAKA DA JANABA:
* ALWALAR MAI JANABA KAFIN BARCI=
= AISHA R/A tace- ANNABI SAW ya kasance idan yanason cin abinci ko yaci abinci alhali yanada JANABA sai yayi tsarki wato yawanke farjinsa sai yayi alwala irinna salla” <BHR & MSLM>
= IBN UMAR yacewa ANNABI SAW- YA RASULALLAH! shin dayanmu zaiyi barcine alhali yanada JANABA? Sai ANNABI yace- E, in yayi alwala, <SHH-ABI DWD,
= ANNABI SAW “mutum 3 MALA’IKU bazasu kusancesu- gawar kafiri, da na mijinda yashafa turaren mata, da mai JANABA sai in yayi alwala” <ABU DWD, AHMD, DAHAWY, BYHQY, TRMZ>
** HUKUNCIN WANNAN ALWALAN:
IMAM NASIRUD-DEEN ALBANY acikin ADABUZ-ZIFAF yace- wannan alwalar ba wajibi bane mustahabbine mai kakkarfa, domin ANNABI SAW yacewa IBN UMAR “yi alwalan in kaso” <IBN HIBBAN>
Da Hadisin AISHA R/A tace- ANNABI SAW yana barci da JANABA ba tareda ya shafi ruwaba sai in ya tashi sai yayi wanka, <IBN ABI SHAIBAH, AS’HABUS SUNAN banda NASA’I, DAHAWY, DAYALISY, AHMD, BAGAWY, ABU YA’ALA>
*** TAIMAMA MADADIN ALWALAN:
SHEIKH ALBANY yace- ma’aurata masu JANABA in sunason kwanciya barci kafin wankar JANABA, madadin alwalar yana iya taimama,
Domin yazo a Hadisin AISHA tace- ANNABI SAW ya kasance idan JANABA yakamashi yanason yayi barci sai yayi alwala ko yayi taimama” <IBN- ABI SHAIBAH, DABRANY, IBN-HAJAR yace- isnadinsa Hasan ne>

YA RABBANA KABAMU TSARKI A DUNIYA A LAHIRA!
AMEEEEEEEEEEN.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website