Khudubar Juma’a – Hattara da mutuwa

[HATTARA DA MUTUWA]

Ya ku ‘yan uwa masu daraja! Ya dacewa mai hankali yaribaci lokutansa kuma yarika kididdigan rayuwarsa kuma yakasance mai kiwatan lokacinsa kuma mai rowan lokacinsa ga duk abinda bazai amfaneshi ba, kada yabata dakika daya a rayuwarsa sai ga abinda zai jawo masa anfani na duniya da barzahu da kuma lahira,

Ya kai Dan uwa mai daraja! Rayuwa da kake gani kalilan ce, kuma ajali kusane, duk dadewa ajali na nan tafe domin dukkan ajali a rubucene,

ANNABI NUHU A/S- wa’azi kadai yayi shekaru 950 yana yi, amma dukda haka da ajali yazo masa aka tambayeshi misalin duniya, Sai yace- kamar wanda yashiga daki ta kofa sai yafita ta wata kofa daban,

Ya kai Wanda ALLAH ya wadatar dashi da koshin lafiya! kuma kana rayuwa acikin wadata da jin dadi, kamaida hankali kanemi guzurin kiyama don mai yiwuwa mutuwa yayima bazata! alhali yayinnan ka dulmaya cikin sakaci da gafala! Sai kaciji yatsan nadama amma kash nadama alokacin batada amfani!

Ya ‘yan uwana musulmai! Lalle jujjuyawar watanni da shekaru tareda nisan kwana ba tabbas bane suzama alhairi, suna iya zama alhairi ga mai ita hakama suna iya zama sharri,
ANNABI SAW yace- “mafi alhari acikin mutane shine wanda rayuwarsa tayi tsawo kuma aikinsa yayi kyau, kuma mafi sharrin mutane shine wanda rayuwarsa tayi tsawo kuma aikinsa yayi muni” {AHMD- 20,415, TRMZ, ALHAKIM}

Ya ku bayin ALLAH! Abin mamakine tayadda a kullum Dan Adam yana ganin ayoyi da alamoninda suke nuna masa cewa shi mai tafiyane kuma mai barin wannan duniyarne! zaiga za’a wuce da gawa a gabansa amma shi bazai wa’azantu ba!
Zaiga gobara ta kama ko hatsarin mota ko girgizan kasa ko yake yake yalakume daruruwan rayuka amma haka zaka shi bazai dauki darasi akan nasa mutuwar ba!

Ya ku gafalallu! Duniyarku gidane na rudu da damuwa da bakin ciki, kuma babu shakka mai karewane, duk wanda yake cikinta zai mutu! Abinda yake wurinku mai karewa ne! Lahira shine madawwamin gida, abinda yake wurin ALLAH mai wanzuwane, mafi girman jahili a mutane shine wanda ya bararda lahirarsa don duniyarsa! TAQAWA shine mabudin farin ciki duniya da lahira!

Ya ku al’ummar ANNABI SAW! mutuwa koface kuma kowa Sai ya shigeta! Akwai ranarda rayuwa zai sauyawa mutum, zaiga abubuwanda bai taba ganinsuba, zaiji sautinda bai taba ji ba, zai yanke alaka da dukkannin mutane yakoma alaka da mala’iku tayin cire rai da zaman kabari!

Ya ku ‘yan uwa! Duk wanda alamomin mutuwarsa suka bayyana agareshi yasani yana fuskantar mawuyacin hali mai tsanani- tunda ANNABI SAW takansa yana watsa ruwa a jikinsa yayin mutuwarsa! Don haka sai yazanto mai hakuri domin shi mutuwa yanada gigitawa kwarai, akwai zafin fitan rai da mayenta da kuma magaginta! Ga zafin rabuwa da dangi da masoya! Ga kuma fargaban makoma da abinda za’a tarar acan!
Kuma yaroki ALLAH kada shedan yahadashi fada da ALLAH, domin shedan zai tara mataimakansa yace- mudage mu batar dashi domin in yakufce mana yanzu yamutu har abada ya kufce mana!
Shi shedan din zai rika zugashi yanace masa- kaga wannan halinda kake ciki na jinya da kuma magagi ALLAH ne yajefaka, wai domin yasa masa kin ALLAH yaki furta Kalmar shahada kuma yamutu yana haushin ALLAH!
Shiyasa ANNABI SAW yake yawan fada a du’arsa= ya ALLAH ina neman tsarinka daga kautarwan shedan yayin mutuwa” {ABU DAWUD}

Daya cikin Magabata yace- naga yawancin mutane abin mamaki idan jinya tadamesu sai su shagaltu da koke koke da neman magani don samun sauki kadai, wannan kuskurene yashagaltu dasu kadai, yanada kyau yashagaltu dasu ammafa yahada da shagaltuwa da gyaran tsakaninsa da mahaliccinsa, yashagaltu karatun Qu’ani da sauran zikirrai da nafilfili da tuba da biyan hakkokin mutane da wasiyya domin koda ya rasa waraka daga wannan cutan sai yamutu zai sami rahamar ALLAH da aljannarsa!!!
Amma idan aka shagaltu da neman magani kadai aka bar kimtsin gamuwa da ALLAH sai mutuwa yazo to anyi biyu babu!!! Ba lafiya ba ba ALJANNA ba!!!
Hakama wanda yake cikin koshin lafiya shima yazauna a kimtse don mutuwa na iya masa bazata yamutu kwatsam ko ta hatsarin mota ko akasin haka!!!

YA RABBANA KAJIKAN MAMATANMU KUMA KABAMU KYAKKYAWAR KARSHE!

Khuduba daga

MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
09/Z-QADA/1437HJRY
12/AUGUST/2016MLDY

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website