Kiwan Lafiya – Zazzabin cizan sauro 3

Assalamu alaikum
Duk kanin godiya suntabbata ga Allaah ubangijin daya haliccemu bisa kaddarawarsa, ya ni’imtamu da lafiya, kuma cikin jarabawarsa ne ya ke jarabtarmu da rashin lafiya, cikin rahamarsa ya samar mana da magunguna kuma suka zama hanyar waraka a garemu.

Allaah kai dadin tsira ga manzon rahama annabi Muhammad (saw) da iyalan gidansa da sahabbansa da wadanda sukabi tafarkinsa har izuwa tashi kiyama,

Bayan haka wannan shirinamu na “Kiwan Lafiya” a wannan makon zamu dorane daga inda muka tsaya a wancan mako

Inda zami bayani akan:-
Hanyoyin kamuwa da zazzabin cizan sauro

Kamar yadda muka sani, saurone yake yada wannan cota

– Idan sauro ya ciji mai kwayar cotan, saiya dauki kwayar cotar daga nan

– Idan kaine mutun nagaba daya ciza saiya sama wannan cotar

– Kwayar cotar sai ta tafi zuwa hantarka, inda zata boye a hantar tsawan wani lokaci

– A lokacin da kwayar cotar ta girma a hantar, saitabar hanta, ta shiga kwayoyin jininka
Alokacin alamumi zasu fara baiyana

Kuma za’a iya kamuwa da kwayar cotar daga:-

– Uwa zuwa Dan da yake Ciki

– Ta hanyar Karin jini, in aka dibi jinin me dauke da cutar aka sama wanda bedashi

– Ta hanyar amfani da allura daya(1) ga mutane biyu, Idan akama mai dauke da cotar allura, sannan akai amfani da wannan allura akama wanda bedashi to shima ze dauka.

Alhamdulillah zamu za linzamin shirinnamu na wannan makon sai Allaah ya kaimu mako maizuwa inda zamu dura daga inda muka tsaya

Gabatarwa
HY kakuri (Abu Sajid)

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website