Matasanmu a jiya da yau 7 – shaye-shaye “F”

Matasanmu a jiya da yau 7

Assalamu alaikum ‘yan’uwa masu al’arka barkarmu da kasancewa a wannan gida (Fitila24) a kuma wannan shiri namu (Matasammu a jiya da yau), shirin dake tattaunawa kan rayuwar matasa, fadakar dasu kan k’alubalan dake fukantarsu, da kuma kokarin shiryar dasu ga tsaftatacciyar rayuwa.

Kar de ku manta a shirinmu na baya, muna bayanine ga daya da gacikin manyan masifun da matasanmu ke fama da ita a yau, wato shaye-shaye, ina da muke jin bayani daga bakin Malaman lafiya.

Shirin namu yana tarene da Dr. Abubakar Bagudu daga Akth kano daga bangaren kula da lafiyar kwakwalwa. In da yake mana bayani akan shaye-shaye

Kuma mun tsayane daidai inda Dr. Zai mana bayane akan, me ake nufi da drug abuse a Hausance?

Cigaba…..

Dr. Idan akace drugs abuse me ake nufi dashi a Hausance?

Zamu iya cewa yana da ma’ana guda uku (3)

I. Ma’ana ta daya itace, dukkan sanda mutum ya sha wata kwoya, yai amfani da ita ba ta yadda aka tsara a yi amfani da itaba.
Misali mafi yawancin mu, mun san benelin ko kuma ince cup syrup, wanda ake sha maganin tari ko kuma mura, toh duk wanda ya sha shi, dan biyan wata bukata, dan ya samu maye a kansa, ko dan ya samu bacci, ko wani abu makamancin haka, toh a wannan lokaci yayi abinda bai daceba, ya zama ya yi abinda muke cewa drug abuse, saboda ya sha shi badan amfanin da aka yi shi dan shi ba.

II. Ma’ana ta biyu itace, duk sanda mutum ya sha maganin da aka bashi a asibiti, fiye da ka’idar likita, shima kayi abusing din shi,
Misali ka je asibiti, an baka maganin da ya ke sa bacci, an ce ka sha shi kwana biyar, sai mutum ya cigaba da sha, sabida yana jin dadinsa, to shima anan yayi abinda ba daidaiba, ka yi abusing dinsa.

III. Ma’ana ta uku itace, wadda babu kwana-kwana, wato shan kwayoyin da dama an haramtasu, duk kan wasu kwayoyi ko wani abu wanda dama an harantama mutum ya sha shi, toh wannan idan mutum ya sha to kai tsaye kayi abusing drug,
Misali kamar ganye ko wiwi kamar yadda muka santa.

To wadannan ma’aunai guda uku, sune duk wanda mutum yai amfani da shi, to yayi abusing drug, da fatan mun gane.

Toh ‘yan’uwa ‘yan-albarka zamu dakata anan sai Allah ya kaimu mako mai zuwa, zamu cigaba daga inda muka tsaya.

Dodiya ta musamma da fatan alheri ga Dr. Abubakar Bagudu daga Akth kano daga bangaren kula da lafiyar kwakwalwa, Allah ya sakawa Dr da alheri bisa kokarinsa na wayar da kan Jama’a

Mu tara a mako mai zuwa tare dani:- H.Y Kakuri (Abu~Sajida)

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website