Mimbarin Juma’a – Abin lura a ruwan sama

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
02/ Z-QADA/ 1437HJRY
05/ AUGUST/ 2016MLDY

TOPIC= [ABIN LURA A RUWAN SAMA]

Na kasashi gida 3:

***** (1) MUQADDIMA *****
Ya ku ‘yan uwa masu daraja! Muji tsoron ALLAH kuma mu kiyaye lokuta muribaceta- domin kiyaye lokuta yana anfanar rayuwa,
Dare da rana suna yin aiki acikinku- na irga kwanakin ajalinku da tsufarku da zuwan kiyama- don haka ku ma kuyi aiki acikinsu ayyuka nagari zakuci riba kuma zaku yabawa kyakkyawar makomarku insha’allahu,
Ya ku ‘yan uwa! Musani sauye sauye da muke gani a rayuwa kuma mukeji- na sanyi ko zafi, dare ko rana, kuruciya ko tsufa, damina ko rani- bai dace murika kyalesu suna shudewaba ba tareda muna lura da kuma tadabburinsuba, musammanma sauyin da muke ciki yanzu na damina, hadari, ruwan sama da tsirrai kada suwuce kamar wasa domin yawancinmu bamwa lura da sakonni da ayoyinda suke dauke dashi.

***** (2) ABUBUWAN LURA GUDA 10 A HADARI *****

1- KADAITUWAR ALLAH:
Mafi girman abin lura acikin hadari da kuma saukar ruwan sama shine- daliline da yake nuna kadaituwar ALLAH da kuma karfin mulkinsa da ikonsa da gudanarwarsa, kuma shi yacancanci abauta masa shi kadai ba tareda hadashi da waninsaba,
=ALLAH SW yace <shin wanda ya halicci sammai da kassai kuma yasaukar muku ruwa daga sama yatsirarda tsirran lanbuna masu ban kayi wanda ku baku isa ku tsirarda itatuwanta ba, shin akwai wani abin bauta tareda ALLAH? bari kawai! su kafirai mutanene masu daidaita ALLAH da wasu> {SRT NAMLI- 60}
=ALLAH SW yace <kace dasu- shin idan ruwanku yawayi gari ya yanke- to waye zaizo muku da ruwa mai bubbuga?> {SRT MULK-30}
Ya ku mutane! Da Mala’iku da Mutane da Aljanu zasuyi taron dangi don su hado hadari su saukarda ruwan sama to wallahi basu isa su saukarda koda digon ruwa ba!!!

2- RUWAN SAMA RAHAMA NE:
zaka ga kwari ya bushe ya zama kura da turbaya! sahara ta tsotse! Gonaki sun kekashe! Sai ALLAH MAI RAHAMA yasauko da sashin rahamarsa, sama tadauki hadari kuma takada tayi ruri! kofofin sama yabudu ruwa masu yawa susauko a dakikai irgaggu! nan take duk inda kaduba ruwane! Kwari yacika da ruwa gar bakin gaba! Sahara yayi shakundum da ruwa! Kwanaki kadan sai kaga tsirrai da ciyayi da ganyayyaki sun lullube ko ina a daji! ALLAHU AKBAR!!!
RUWA RAHAMANE NA ALLAH!
BABU WANDA YAKAI ALLAH KYAUTA!
BABU KYAUTANDA YAKAI KYAUTAN ALLAH!
=ALLAH SW yace <shine wanda yake saukarda ruwan sama bayan mutane sun cire tsammani sai yawatsa rahamarsa, shine majibinci kuma godadde> {SRT SHURA-28}

3- YIWA ALLAH KYAKKYAWAR ZATO:
Saukan ruwan sama yana daga abinda yake nuna yiwa ALLAH kyakkyawar zato kuma da sanin girman fadin rahamarsa,
=ANNABI SAW yaga wata mata ta rungume karamin yaronta,
sai yacewa SAHABBAI R/A “shin a ganinku matannan zata jefa yaronnata a wuta?
SAHABBAI R/A sukace- a’a
Sai ANNABI SAW yace ” ALLAH SW yafi tausayin bayinsa sama da yadda matannan take tausayin yaronta!” [SHH BHR-5999 & SHH MSLM-2754]
ALLAHU AKBAR!
Nawane wadanda dasafe sun yanke tsammani daga samun ruwa saboda jinkirinsa? Amma daga baya kaga ruwa safe da yamma!
YA mai tarin damuwa!
YA wanda yake fama da jinya har shedan yasashi yanke tsammani daga waraka!
YA wanda yake fama da zunubi har shedan yasashi yanke tsammani daga yafiya!
Kaguji yanke tsammani!
Kakoma karoki ALLAH!
Ka kyautata masa zato!
ALLAH zai yayema dukkan damuwa!

4- TSORATARWA TA ARADU DA WALKIYA:
Acikin abin lura da tadabburi a damina shine mutum yasani akwai gomnatinda take masa tsawa a sama da kuma jiyar dashi tasbihan halittun sama! Duk karfin tsawarsa tsawan aradu yafi nasa! Don haka ALLAH yana jiyarda Dan Adam amo da rugugin aradu da karfin hasken walkiya don tauna tsakuwa aya taji tsoro!!!
=ALLAH yace <kuma aradu yana tasbihi da hamdala gareshi hakama mala’iku suna tasbihi da gode mishi kuma yana turo tsawawwaki sai yakashe wanda yaso da ita yayinda suke jayayya akan lamarin ALLAH, kuma shi mai tsananin hila ne> {SRT RA’AD-13}
=ALLAH yace <ko kuma kamar hadarine daga sama acikinsa akwai duffai da tsawan aradu da walkiya suna toshe kunnuwansu da yatsunsu don tsoron mutuwa……….. Saura kiris walkiyar yamakantar dasu> {SRT BQR- 19-20}

5- FADAKARDA RAFKANANNE:
=ALLAH SW yace <lalle hakika mun sarrafashi domin tunatarwa, amma yawancin mutane sunki sai yawan kafirci> {SRT ISRA’I-89}
=ALLAH SW yace <shin kunga ruwanda kuke sha? Shin ku kuka saukar dashi daga hadari ko mu muke saukarwa? Da munso da mun sanyashi gurbatacce donme bazakuyi godiya ba? {SRT WAQI’AH-68-70}

6- DALILINE DAYAKE ISHARA GA TADA MUTUM BAYAN MUTUWARSA:
=ALLAH SW yace <yana daga ayoyin ALLAH zakaga kasa a kekashe idan muka saukarda ruwa akanta sai ta motsa ta kumbura, lalle Wanda yarayata tabbas zai rayarda matattu, lalle shi mai ikone akan dukkan komai> {SRT FUSSILAT- 39}
=ALLAH SW yace <ALLAH shine wanda yake turo iska sai tamotsa hadari sai mukora hadarin zuwa ga matacciyar kasa sai murayarda kasar bayan mutuwarta, kamar hakane zamu tada matattu> {SRT FATDIR-9}

7- GANE ANYI ZUNUBI DOMIN TUBA:
Rashin ruwa sakone mai zaman kansa dayake nuna mutane suna sabawa ALLAH, tuba da istgfari sune zasu kawarda zunubban kuma sudawo da ruwan sama,
=ALLAH SW yace akan harshen ANNABI NUHU A/S <kunemi gafarar Ubanginku lalle shi mai gafarane* zai saukarda ruwan sama akanku ganga ganga> {SRT NUH- 10-11}

8- NUNA RASHIN AMINTUWA DAGA AZABAR ALLAH:
Hadari alamane da yake nuna ALLAH fa ashirye yake yasaukarda azaba aduk lokacinda yaso, domin anyi wasu al’ummu a baya da ALLAH ya halakar dasu da hadarin ruwa,
=ALLAH yana maganar yadda ya halakarda ADAWA yace <lokacinda sukaga hadari ya fuskanci kwarinsu Sai sukace ga hadari zaiyi mana ruwan sama, Sai ALLAH yace ba haka bane, wannan abinda kuke neman gaggawan zuwansane, iskane acikinta akwai azaba mai radadi* tana rugurguza kowane abu da izinin ubangijinsu sai suka wayi gari babu abinda za’a gani sai gidajensu kawai, kamar hakane zamu rika sakayya akan masu laifi> {SRT AHQAF-24-25}

9- RIBATAR LOKUTAN KARBAN ADU’A:
=ANNABI SAW yace “lokuta biyu ba’a mayarda adu’a, 1- yayin kiran salla, 2- yayinda ruwan sama ke saukowa” {SUNAN ABI DWD-2549, DARIMY-1200, ALHAKIM, ALBABY YA HASSANA}

10- SADARWAN NI’IMAR ALLAH GA BIYINSA KAI TSAYE:
Ni’imomin ALLAH ya banbanta da na bayinsa, yanzu da shugaban kasa ko gomna zai bawa talakawa takin noma ko abinci to bazai bayar da kansaba saidai yawakilta wasu sai su tsakura, suma su wakilta wasu suma su tsakura, a haka a haka har kadan daga ciki ya isowa kadan daga talakawa, wanin talakanma sai yabada cin hanci,
Amma kadubi ALLAH SW kai tsaye yake sadarda hasken rana da wata zuwaga bayinsa babu banbancin talaka da mai kudi, haka yake saukarda ruwa kai tsaye a gonakan talakawa da masu kudi babu banbanci, zaka ga talakawa suna layin karban taki amma baswa yin layin neman ruwan sama, kai tsaye ALLAH yake isar musu har gonakinsu da gidajensu,
ALLAHU AKBAR!
Ruwan same kenan!
Kyauta daga ALLAH kai tsaye!
Zuwa ga bayinsa kai tsaye!

***** (3) RUFEWA *****
Ya ku bayin ALLAH murika yiwa ALLAH SW godiya na baka da aiki,
=ALLAH SW yace <ubangiji yabada shela idan kun gode zan kara muku>
Don haka muyi anfani da wannan dama na ni’imar ruwan sama muyi noma don musami ni’imomin abinci,
Kuma duk lokacinda kazo shiga gonarka kace
ما شاء الله لا قوة إلا بالله
MA SHA’ALLAHU LA QUWWATA ILLA BILLAH,

YA ALLAH! muna maka godiya akan zaman lafiya da kabamu a yankunanmu, muna rokonka kakara mana zaman lafiya a dauka cin 9jry kabamu abinci da arziki da cikakken IMANI da kyakkyawar cikawa a duniya da kuma FIRDAUSI a lahira!!!
Amiiiiiiiiiiiin.

Tare da:- Shik Abubakar bin Mustafa Barno

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website