Mimbarin Juma’a – Ashura

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
05/MUHARRAM/1438HJRY
07/OCTOBER/2016MLDY

TOPIC= [ASHURA]

***MABUDI:
MALAMAN TAFSIRI sunce= lokacinda FIR’AUNA da rundunarsa suka fito don bin ANNABI MUSA A/S da mabiyansa don sukamosu su azabtar dasu, rundunane mai karfin gaske da kuma yawan gaske, har wasu sukace rundunar sun kai 1,600,000- ALLAHU A’ALAM,
ANNABI MUSA A/S da msbiyansa sun iso bakin teku da dare saidai ba damar wucewa saboda dandazon ruwa gagara misali,
Can da safe sai ga FIR’AUNA da dandazon rundunar tasa suma sun doso bakin ruwan, sunyi ido biyu da ANNABI MUSA A/S da mabiyansa, sunga juna kuma kowa yaga kowa, ba shakka ba tantama mutanen ANNABI MUSA A/S sunga halaka, cikin halin tsoro sukace=
<<< lallemu tabbas za’a riskemu >>> SRT-SHU’ARA-61
Sai KALAMULLAHI MUSA A/S yace musu=
<<< a’aha! Lalle UBANGIJINA yana tare dani sai shiryar dani- mafita >>> SRT-SHU’ARA-62
ALLAHU AKBAR!!! kalmace ta neman agaji mai karfi! Kuma cike yake da tabbatuwa da tsabati da yarda da alkawarin ALLAH!!!
FIR’AUNA da rundunarsa suna kara matsowa da kusantowa, tsoro yana kara lullube mutanen ANNABI MUSA! Sai ALLAH yace=
<<< sai mukayi wahayi zuwaga MUSA cewa kabugi kogin da sandarka, sai kogin yatsage 2 sai kowane tsagi yakasance kamar fallen dutse mai girma >>> SRT-SHU’ARA-63
ALLAHU AKBAR! HMMM RUWA ya tsage yazanto tamkar DUTSE!!! Don umurnin ALLAH mai cewa- kasance- sai yakasance,
ANNABI MUSA A/S da mutanensa cikin mamaki da farin cikin mafitar UBANGIJI suka keta busashshiyar hanya atsakiyar kogi suka ketara,
Suna ketarawa kenan FIR’AUNA ya iso da rundunarsa, ANNABI MUSA A/S yaso yasake buga ruwan da sandarsa don hana FIR’AUNA da rundunarsa shigewa hanyar kogin sai ALLAH yahanashi yace masa=
<<< kabar tekun a rabe, lalle su rundunane abar nutsarwa >>> SRT-DUKHAN-24
Lokacinda FIR’AUNA YAGA abinda yagani na hanya atsakitar kogi kuma dukda taurin kansa yasan wannan daga ALLAH ne hakan baisa ya daddara ya kyalesu ya komaba, zuciyarsa tafizgeshi yakutsa hanyar cikin kigin, da rundunarsa sukaga haka suma sai suka kutsa abayansa cikin gaggawa, bayan sun kutsa ciki dukkansu yayinda na farkonsu yake gab da fitowa sai ALLAH SW ya umurci ANNABI MUSA yabugi ruwan da sandarsa akaro na 2, yana bugawa sai ruwan yadawo yanutsarda FIR’AUNA da mutanensa yahallakar dasu ba wanda ya tsira, ALLAH yace=
<<< muka tseratarda MUSA da wadanda suke tare gaba daya * sa’annan muka nutsarda wancan bangaren * lalle acikin wannan akwai aya…. >>>
* * *
ALLAHU AKBAR!!!
Wadannan manyan abubuwan ban mamakin sun farune aranar 10/MUHARRAM, RANAR ASHURA!!!
Yazo da babban darihi kuma yashude yabar mana dimbin darussa da fa’idoji, kadan daga ciki=
* tunatarwa gameda ni’imomim ALLAH da godiya
* ALLAH baya kawo dauki sai an yunkura
* zalunci baya dawwama
* wahala yanada karshe
* taimakon ALLAH yana tareda waliyyansa
* nau’intuwar ni’imomin ALLAH, ni’ima yakan zama azaba hakama akasin haka, dubi yadda ruwannan yazama ni’ima wa su ANNABI MUSA yazama azaba kuma gasu FIR’AUNA,

*** BIDI’O’IN ASHURA DA KUMA ABINDA YADACE A SUNNA:

*IMAM IBN RAJAB ALHANBALY yace=
Amma rikan ranar ASHURA a matsayin ranar bakin ciki da alhinin mutuwa kamar yadda RAFIDAI <YAN SHI’A> sukeyi wai domin an kashe HUSSAINI R/A- wannan yana daga acikin wanda yake bata lokacinsa akan shirime ya dauka yana aiki mai kyau ne, domin ALLAH SW hakama ANNABI SAW basu bada umurnin ariki ranarda wasu masifu suka sami ANNABAWA ko ranar mutuwarsu amatsayin ranar bakin ciki da alhini ba, to ta yaya zakayi haka ga wanda bai kai ANNABAWAN ba??? (لطائف المعارف)

Hmmmmm!
Kaima Barafide in ba jahilcinka da iskancinkaba ai ihun mutuwa da kururuwarsa babu kyau, tunda har ANNABI SAW cewa yayi wanda yayi hakan zai shiga wuta kuma Wanda akayiwa hakan za’a azabtar dashi!!!
Kuma ai ANNABI SAW yaga wata tana kuka akan makabarta yakwabeta har yake cewa الصبر عند الصدمة الأولى

* SHEIKH ABDUL’AZIZ IBN MUHD IBN ABDULLAHI ASSADHAAN yace=
Kungiyoyi daban daban sunada sabanin nazarinsu akan ranar ASHURA,
=YAHUDAWA suna girmama ranar ASHURA kuma suna rikansa ranar biki harma suna tufatarda matansu sabbin kaya da gwalagwalai
= TSIRARUN RAFIDAI suna daukan ranar ASHURA ranar makokin mutuwa da bakin ciki wai don HUSSAINI R/A an kasheshi aranar, suna wasu rubuce rubucen karya wacce alkalami yake kunyar rubutawa
= NAWASIBAI suna farin ciki awannan rana ta ASHURA don dariya da jin dadin an kashe HUSSAINI,
Wadannan dukka uku akan bata suke,
Amma sai ALLAH SW yashiryarda Musulmai zuwaga gaskiya sai suke azimtar yinin ASHURAN don kwaikwayon ANNABI SAW basu karata da wasu bidi’o’in wadancanba wanda ALLAH bai saukarda dalili akansuba,
Wadannan su sukayi daidaidai domin hadisin ABDULLHI IBN ABBAS R/A yace- ANNABI SAW yazo MADINA sai yatararda yahudawa suna azumi, Sai yace- “azumin me haka?”
Sukace- wannan shine ranarda ALLAH ya tseratarda Bani isra’ila daga makiyinsu Sai MUSA ya azumceshi,
Sai ANNABI SAW yace- “na fiku cancantar kusanci da MUSA” Sai ya azumceshi kuma yayi umurni a azumceshi, [BUHARI-2004, MUSLIM-1130]
ANNABI SAW yace “azumin ASHURA yana kankare zunubin shekara guda a gabanninsa” [MUSLIM-1162]
Don haka azumtar ASHURA akeyi don godiya wa ALLAH, ai ANNABI SAW ya karantarda sunnar ASHURA tunma ba’a haifi HASSAN R/A ba ballantana ma HUSSAINI R/A,

Ya Dan’uwana! Kaji falalar azumin ASHURA! kuma ASHURAN wannan shekaran zai kama yinin larabannan mai zuwa- don haka kada kayi kasa a gwiwa kai da iyalanka ku azumceta, kumori wannan daman don kakkabe nauye nauyen zunubbanda aka diba wanda bamusan iyakantaba a shekararda yagabata,
= RUBAY’U BINTUL MU’AWWIZ tace- muna azumtar ASHURA kuma munasa kananan yaranmu suma su azumceta, idan dayansu yayi kuka sai mubashi bebin wasa har yakai lokacin buda baki”

*** YADDA ZAKA AZUMCETA:
=IBN SEEREEN da AHMAD sunce- Wanda zai azumta ya azumci ranar 9 da 10 saidai in kwanan watan ya rikice masa sai ya azumci kwanaki 3, [,IQTIDA’U SIRATDIL MUSTAQEEM]
=in ka azumceta gaba daya uku yafi, wato ranakun 9, 10, 11, domin sake samun karin ladan hadisinda ANNABI SAW yace “azumi 3 akowace wata daidaine da azumtar watan” [QISMUL FIQ’HI, LIQAAHAATUL BABIL MAFTUH]
=Ana iya azumtar 9, 10
=Ana iya azumtar 10, 11
=IBN TAIMIYYAH yace- Ana iya azumtar 10 kadai babu karhanci akan hakan, [AL’IKHTIYAARAAT]

***ADU’A:
RABBANA KASA MUWANYE KAFIYA DA KUMA IMANI!
Amiiiiiiiiiiiiiiin.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website