Mimbarin Jumma’a – Bautan Allah (SWT)

Assalamu’alaikum warahmatullahi wa barakatuhu.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya azurtamu da lafiya, kuma ya sanyamu daga cikin wadanda suka halarci wannan wata mai albarka (Ramadan) cikin rayuwa da lafiya, tsira da amincin Allah su tabbata ga babban jakadan Allah, manzan Rahama annabi Muhammad S.A.W

Bayan haka a yau wannan shirin namu (Mimbarin Juma’a) ya lekane Babban Masallacin Juma’a na unguwar Kakuri, karamar hukumar Kaduna ta kudu, a nan jihar Kaduna, in da muka saurari Khuduba daga bakin babban limain Masallacin, Sheik Muhammad Sani Imam inda ya mana Khuduba kamar haka….

Bayan godiya data gabata ga Allah bisa ni’imarsa da yayi a garemu, Malam ya yi kira ga al’umma da su zage dantse cikin bautawa Ubangijinsu musamman a wannan wata mai alfarma (Ramadan), sannan Malam ya janwo hankalin al’umma kan tarawihi, in da ya bayyana nassoshi da fa’ida kan tarawihi, sannan ya bayyana sabanin adadin raka’o’in tarawihi tun daga kan sahabbai, zamani bayan zamani, har izuwa yau …
Bayan haka malam ya yi kira ga al’umma da kar sudau wadannan banbancin adadin raka’o’i, wata mas’alar da zata kawo sabani a tsakaninsu, ya bayyana cewa duk yardar Allah ake nema, sannan ya yi kira ga al’umma da su sanya ikilasi cikin yaiyukan ibadarsu …

Daga karshe malan yayi addu’ar neman lafiya da kariyar Allah ga shugaban kasarmu (Nigeria) Muhammad Buhari, sannan Malam ya yiwa kasarmu addu’r zaman lafiya, da sauran kasashen yan’uwa Musulmai …

Muna addu’a abinda Malam ya roka Allah ya karba, Allah ya karbe idabarmu amin summa amin …
Sai mun ji daga kareku, wacce Khuduba limaminku ya muku a anguwarku, ko inda kai Sallah …

A madadin wannan gida Fitila24 sai kuma ni dana shirya na gabatar nakecewa mu tara a mako mai zuwa dan jinmu dauke da wani saban shiri …

Domin samun damar cin moriyar shirye-shiryan Fitila24.com sai ku biyomu a babbar shafinnmu a adireshi kamar haka www.fitila24.com sai kun zo ….

Daga:- Hassan Y Kakuri

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website