Mimbarin Juma’a – Falalar Ciyarwa a watar Ramadan

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi mana umarni da aikata kyawawan aiyuka, dan ya saka mana da kyakykyawan sakamako. Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzan rahama Muhammad S.A.W.

Bayan haka a yau wannan shirin namu (Mimbarin Juma’a) ya lekane Babban Masallacin Juma’a na unguwar Kakuri, karamar hukumar Kaduna ta kudu, a nan jihar Kaduna, in da muka saurari Khuduba daga bakin babban limain Masallacin, Sheik Muhammad Sani Imam in da ya mana Khuduba kan muhummancin ciyarwa (sadaka) musamman a wannan wata mai albarka (Ramadan) ….

Malam ya fara da janyo hankali da Hadisan Manzan Allah S.A.W, wadanda suke nuna fifikon yin sadaga a watan Ramadan …

* Hadis “Mafificin Sadaka itace wacce akayi a watan Ramadan”
* Hadis “Duk wanda ya ciyar da mai Azumi, za’a baci sakamakon (lada) Azumin wanda ya ciyar, kuma ba tare da an rage masa komai ba, a nashi sakamakonba (shi wanda aka ciyar).

Sannan Malam ya cigaba da kawo ayoyi da suke kwadaitarwa kan aiyukan alheri.

Bayan wannan Malam ya janyo hankalin al’uma kan su yi amfani da damar wadata da Allah ya musu wajan ciyarwa da sauran aiyukan alheri, tun kafin damar ta kubuce musu.

Daga karshe malan yayi addu’ar neman lafiya da kariyar Allah ga shugaban kasarmu (Nigeria) Muhammad Buhari, sannan Malam ya yiwa kasarmu addu’r zaman lafiya, da sauran kasashen yan’uwa Musulmai …

Muna addu’a abinda Malam ya roka Allah ya karba, Allah ya karbe ibadarmu amin summa amin …

Sai mun ji daga kareku, wacce Khuduba limaminku ya muku a anguwarku, ko inda kai Sallar Juma’a …

A madadin wannan gida Fitila24 sai kuma ni dana shirya na gabatar nakecewa mu tara a mako mai zuwa dan jinmu dauke da wani saban shiri …

Domin samun damar cin moriyar shirye-shiryan Fitila24.com sai ku biyomu a babban shafinnmu a adireshi kamar haka www.fitila24.com sai kun zo ….

Daga:- Hassan Y Kakuri

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website