Mimbarin Jumma’a – Ban-kwana da Ramadan

Assalamu alaikum jama’a barkarmu da sake saduwa a wannan rana ta Jumma’a, a kuma wannan gida namu mai albarka (Fitila24), a kuma wannan shiri namu na Mimbarin Juma’a. Ina da muke kawo muku abinda ya saukaka daga khudubar Jumma’a.

Yau wannan shirin namu (Mimbarin Juma’a) ya ziyarci Babban Masallacin Juma’a na unguwar Kakuri, karamar hukumar Kaduna ta kudu, a nan jihar Kaduna, in da muka saurari Khuduba daga bakin babban limain Masallacin, Sheik Muhammad Sani Imam.
Shehin Malamin ya mana Khuduba ne kan abin da ya gabata na falalar Ramadan da kuma abinda ya kamata mu biyo da shi a bayan Ramadan …

Bayan godiya ga Allah S.W.T da salati ga fiyayyan halittah manzan rahama Muhammad S.A.W, da yabo da jinjina ga iyalanda da sahabbansa.

Malan ya fara da nusantar da jama’a irin falala da albarkar da ake samu cikin watan Ramadan, tare da tabbatar da lallai wadanda su ka yi aikin ibada da ikilasi a cikinsa (Ramadan), sun samu lada da riba sama da wadanda su ka samu riba akan kasuwanci cikin Azumi ko yayin hidimar sallah …

Malam ya ci-gaba da cewa amma abin takaici sai ka samu wasu har kosawa su ke yi da Azumin, dan kawai su koma ga abinda suke aikata, wasuko kwadayi suke a ci-gababa kawai dan ribar da suke samu a kasuwancin su …

Malam ya ci-gaba da cewa hakika hakika ribar da ake samu a wannan wata wajan aiyukan ibada tafi kowacce kasuwanci, domin idan mutum yai sallar nafila na bashi lada tamkar ta farillah, idan kuwa mutum yai ta farillah ana ninka (rubanya) masa sau saba’in …

Sannan Malam ya bayyana cewa yana daga cikin alamun Allah ya amshi ibadar mutum cikin Ramadan, mutum ya dore da yaiyukan alheri a bayan watan Ramadan din …

Malam ya ci-gaba da cewa magabata na kwarai sukan dauki tsawan wata shida suna addu’a kan Allah ya amsa musu ibadar da suka gabatar a Ramadan …

Bayannan Malam ya bayyana falala da muhimmancin Azumi shidda a wannan wata da muke ciki (Sitta Shawwal), in da Malam ya karanto nassi daga manzan Allah S.A.W in da yake cewa “duk wanda ya azumci Ramadan sannan ya biyo da Azumi shida a cikin Shawwal, to tamkar ya azumci shikarane” Hadis. Wanda ko ya dawwama duk bayan Ramadan yana Azumi shida a Shawwal toh tamkar yayi duk rayuwarsane cikin Azumi …
Daga karshe Malam ya yi addu’ar alheri ga al’umma …

Muna addu’a abinda Malam ya roka Allah ya karba, Allah ya karbe ibadarmu amin summa amin …

Sai mun ji daga kareku, wacce Khuduba limaminku ya muku a anguwarku, ko inda kai Sallar Juma’a …

A madadin wannan gida Fitila24 sai kuma ni dana shirya na gabatar nakecewa mu tara a mako mai zuwa dan jinmu dauke da wani saban shiri …

Domin samun damar cin moriyar shirye-shiryan Fitila24.com sai ku biyomu a babban shafinnmu a adireshi kamar haka www.fitila24.com sai kun zo ….

Daga:- Hassan Y Kakuri

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website