Mimbarin Jumma’a – Yaya halinmu yake a bayan Ramadan

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
06/SHAWWAL/1438HJRY
30/JUNE/2017MLDY

TOPIC= [[YA YA HALINMU YAKE BAYAN RAMADAN?]]

***MATASHIYA:
ALLAHU AKBAR! Mun kasance a jiya jiyannan muna jiran WATAN RAMADAN, To RAMADAN yazo har ya wuce tamkar walkiya, hakama duk abinda zaizo sai yazo, kowane ajali arubuce yake!
ALLAHU AKBAR! yini yana bin dare, wata yana bin wata! shekara yana bin shekara!
=ALLAH yace- (ALLAH yana jujjuya dare da rana, lalle acikin wannan akwai abin lura ga masu basira) {SRT NUR}
=ALLAH yace- (wadannan kwanakine muke jujjuyashi ga mutane domin ALLAH yabayyana muminai masu aiki na kwarai kuma yariki shahidai acikinsu) {SRT ALI-IMRAN-140}
ALLAHU AKBAR! Watan RAMADAN ya juya baya, bamu san zamu ga wata RAMADAN din ko bazamu ganiba, (kace lalle iliminta yana wurin ALLAH, UBANGIJINA baya bata kuma baya mantuwa) {SRT TDAHA-52}
Ya ku ‘yan uwa! Sanannene yawancin musulmai awatan RAMADAN suna kokari wajen ayyukan alhairai da gaggawa zuwa gareta da barin zunubi da guje mata, ba shakka wannan alamace ta alhairi da albarka, wannan matashiyar shi yazunguro tambaya mai taken= YA YA HALINMU YAKE BAYAN RAMADAN???

***MUTANE SUN KASU GIDA 3 A MU’AMALARSU DA RAMADAN:
(1) mutanene nagari masu imani da taqawa tun kafin zuwan RAMADAN, da zuwan RAMADAN sai yakara musu imani da taqawa da son dukkan nau’ikan alhairai, kamar azumi, sadaka, salloli, karatun Qur’ani da sada zumunci, sun rabauta da nagarta kafin RAMADAN da bayanta, wadannan sune fiyayyun mutane a kashe kashennan guda ukun,
(2) mutanene nagari kafin RAMADAN saidai suna fama da aikata wasu zunubbai, amma da zuwan RAMADAN sai tayi tasiri akansu suka daina aikata zunuban acikinta kuma sukayi alkawarin barin aikata zunubban harma bayan RAMADAN, wadannan in sun tabbata akan wannan niyyar da sannu zasuga abinda zai faranta musu, don sune suke bin kashin farko
(3) mutanene na banza marasa kirki da RAMADAN yazoma basu sauya haliba kuma batayi musu tasiriba suka cigaba da futsara da shashanci a RAMADAN kuma suka laptawa kansu nau’ikan zunubbai sukayi asarar makudan lada, wadannan sunfi kowa asara, muna musu nasiha suji tsoron ALLAH WALLAHI MUTUWA TANA ZUWA!!!

***YA YA YADACE MUZANTO BAYAN RAMADAN???
Ya ku Musulmai! Lalle daga ni’imominda ALLAH SW yayi mana shine yawaita mana yanayi masu falala dayawa wacce yake yawaita makudan lada acikinsu, cikin wadannan lokutan akwai watan RAMADAN wacce ta nannade tabarmarta a kwanakinnan, ALLAH YAKARBA MANA!
Ya ku bayin ALLAH! Don watan RAMADAN ya wuce- tofa ALHMDLH ibada bai wuceba yana nan har zuwa mutuwa!
Idan watan RAMADAN da aka saukarda QUR’ANI acikinsa ya shude- tofa ALHMDLH karatun QUR’ANI tana nan har mutuwa!
Idan tarawihi da tahajjudi sun wuce- tofa ALHMDLH KIYAMULLAILI na nan har mutuwa!
Idan azumin RAMADAN ya wuce- tofa ALHMDLH azumi na nan har mutuwa!
Cikin azumin akwai azumi guda 6 a wannan wata da muke ciki na SHAWWAL wanda ake yinsa a matsayin godiya ga ALLAH daf bayan RAMADAN akan damanda yabayar na azumtarta da kuma koyi da ANNABI SAW,
=ANNABI SAW yace “Wanda ya azumci RAMADAN kuma yabiyo da guda 6 a SHAWWAL tamkar ya azumci shekara” (MSLM-1164)

***WASU MAS’ALOLI MASU ALAKA DA AZUMIN SITTA SHAWWAL:
=wani in yasha azumi kamar 1 ko 2 ko 3 a RAMADAN sai yabiyasu a watar SHAWWAL, sai bayan ya kammalasu in yaga yakasa kammala SITTA SHAWWAL sai yadawo yace ya canza niyyar yanzu wancan bashin ya maida ita SITTA SHAWWAL ko yayi akasin haka, yin hakan kuskurene bai halattaba,
=masu cewa yinsu ajere yafi yinsu a yayyanke lada ko akasin haka, kuskurene don babu nassinda yatabbatar
=masu cewa yinsu daf bayan ranar idi yafi falala, hakama a gomar farko yafi na goma nabiyu falala, nagoma na biyu yafi na goma na uku falala, wannan maganace maras dalili,a dukkansu akwai alhairi,
Saidai fa duk da haka gaggauta yinsa shi yafi a BABIN GAGGAUTA AIKIN ALHAIRAI,
=ALLAH ya umurcemu da haka yace (kuyi rige rigen alhairai)
=ALLAH ya yabi ANNABAWANSA wadanda sune zababbun bayinsa da gaggauta ayyukan alhairai- yace (lalle su sun kasance suna gaggautawa cikin alhairai) {SRT ANBIYA’I-90 & SRT MUMINUN 61}
=ALLAH ya umurcemu da haka muma- yace (kuyi rige rige zuwa ga wata gafara daga UBANGIJINKU da wata ALJANNA wacce fadinta tamkar sammai ne da kassai an tanadar da ita ga masu taqawa) {SRT ALI-IMRAN- 133}
=ANNABI SAW yace “abi a hankali akowace abin alhairi saidai in acikin aikin lahirane- to fa a gaggauta” [SNN AB DWD-4810, BHQ a SHU’ABIL IMAN-8461, HKM, ALBANY a SILSILATUS SAHEEHA-1794}
IMAMU TDAYYIBY yace- ma’anarsa= su al’amurran duniya babu tabbacin nasara aciki, meyiwuwa tazanto da kyawun karshe ko munin karshe- shiyasa akeso kabisa a hankali, amma al’amarin lahira wato ibada tanada tabbacin nasara da kuma kyakkyawan karshe ga duk wanda ya aikata bisa ihlasi da kuma dacewa da SUNNA,

***ADU’A:
πŸ‘πŸ»YA RABBANA KASAMU CIKIN MASU DAWWAMA CIKIN TSORONKA DA BAUTA MAKA HAR ZUWA KARSHEN NUMFASHINMU,
πŸ‘πŸ»YA RABBANA KASAMU CIKIN MASU GAGGAUTAWA ZUWA GA AYYUKAN ALHAIRAI DA IHLASI DA KUMA DACEWA DA SUNNAR ANNABINKA SAW
πŸ‘πŸ»YA RABBANA KATSERATAR DAMU DAGA DUKKAN AZABA DON RAHAMARKA,
πŸ‘πŸ»YA RABBANA KASHIGAR DAMU ALJANNAH DON FALALARKA,
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website