Mimbarin Jumma’a – Zakkar fidda kai

 

Assalamu alaikum jama’a barkarmu da sake saduwa a wannan rana mai ta Jumma’a, a kuma wannan gida namu mai albarka (Fitila24), a kuma wannan shiri namu na Mimbarin Juma’a. Ina da muke kawo muku da abinda ya saukaka daga khudubar Jumma’a.

Yau wannan shirin namu (Mimbarin Juma’a) ya ziyarci Babban Masallacin Juma’a na unguwar Kakuri, karamar hukumar Kaduna ta kudu, a nan jihar Kaduna, in da muka saurari Khuduba daga bakin babban limain Masallacin, Sheik Muhammad Sani Imam.
Shehin Malamin ya mana Khuduba ne kan Zakatul Fidir (zakkar fidda kai) da kuma jan hankali kan hakkin Iyaye da ‘yan’uwa …

Bayan godiya ta gabata ga Allah S.W.T da salati ga farin jakada manzan rahama annabinmu Muhammad S.A.W …

Malam ya ‘kara da jadda godiya ga Allah wanda Ya shiryar da mu ta harshen manzanSa ga hanyoyin samun yardarSa (Allah), daganan sai Malam ya cigaba da bayani kan girman hakkin Iyaye, Malam yayi kira ga jama’a kan karsu shagaltu da hidimar iyalai su manta da iyayensu wajan hidindimun Sallah, malam ya cigaba da kira kan kyautatawa iyaye, yi musu dinkin Sallah da abincin Sallah, tare da taimakawa yan’uwa da sauran mabukata. Malam ya bayyana hadarin dake cikin fifita iyali kan iyaye …

Sannan malam ya cigaba da bayani kan wajabcin Zakatul fidir (zakkar fidda kai), malam ya bayyana cewa zakkar fiddakai wajibine, sannan ya bayyana cewa Allah ya wajabtawa al’umma wannan zakkah ta harshen manzanSa S.A.W.

Malam ya kara da cewa wasu jama’ar sukan shagaltu da hidimar sallah su manta za wannan wajibi. Malam ya janyo hankali matuka kan kulawa wajan sauke wannan hakki (zakkar fidda kai).

Malam ya karanto Hadisin manzan Allah S.A.W in da yake cewa ” Dukkan al’ummata zasu shiga al’jannah sai dai wanda yaki, sai sihabbai suka ce, wa ze ki ya manzan Allah, sai manzan Allah S.A.W yace wanda ya min biyya zai shiga aljannah wanda ko ya sabamin toh shine ya ‘ki” *Hadis.

Daga karshe Malam yai addu’ar fatan alheri ga al’umma …

Muna addu’a abinda Malam ya roka Allah ya karba, Allah ya karbe ibadarmu amin summa amin …

Sai mun ji daga kareku, wacce Khuduba limaminku ya muku a anguwarku, ko inda kai Sallar Juma’a …

A madadin wannan gida Fitila24 sai kuma ni dana shirya na gabatar nakecewa mu tara a mako mai zuwa dan jinmu dauke da wani saban shiri …

Domin samun damar cin moriyar shirye-shiryan Fitila24.com sai ku biyomu a babban shafinnmu a adireshi kamar haka www.fitila24.com sai kun zo ….

Daga:- Hassan Y Kakuri

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website