Minbarin Juma’a

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
16- Z/QADA- 1437HJRY
19- AUGUST- 2016MLDY

TOPIC= [JAN KUNNE MARASA LAFIYA]

Na kasa khudubata KASHI 3=

***** KASHI NA-1 *****
MUQADDIMA=
Ya Danuwa mai daraja, abubuwa biyune suka ginu suka zama Mutum,
1- RUHI
2- GANGAN JIKI
Shi RUHI yana matsayin bakonda yakawo maka ziyara ta musamman, shi kuma GANGAN JIKI yana matsayin abin hawanda 🐪🐎 bakon yahau yazo,
Mai hankali shine wanda yakarrama bakon da abin hawannasa ammafa yafi fifita bakonnasa akan abin hawan, yayinda shi mara hankalin yafi fifita karrama abin hawan akan bakonnasa,
Don haka kafifita kulawa da RUHINKA samada kulawa da gangan jikinka,
Ita RUHI kulawa da ita shine rayata da IMANI, TAQWA, TAUHIDI da sauran ibadoji, yayinda shi GANGAN JIKI kulawa dashi shine kulawa da ABINCI, ABIN SHA, MAGUNGUNA da kuma SUTURU,
Kiyaye RUHI kariyace daga dukkan masifa da kuma samun sa’ada na dindindin kuma har abada!!!
Yayinda kiyaye GANGAN JIKI kariyace da sa’ada na lokaci kankani kuma mai Yankewa!!!
Don haka kiyaye RUHI ake gabatarwa samada kiyaye GANGAN.

***** KASHI NA 3 *****
ABUBUWA 10 DA BASU HALATTA GA MARAS LAFIYA BA:
Ya kai maras lafiya! Na kiyaye dokokin ALLAH da iyakokinsa a halin jinyarka, kuma kada radadin jinya da zoginta ta kautar dakai daga hanyar ALLAH da kuma keta iyakokinsa, domin mai yiwuwa kamutu a wannan jinyar sai kayi asarar duniyarka da lahirarka!!
Ga abubuwa 10 da basu halattanba musammanma ga maras lafiya=

(1) YIN MAGANI DA HARAMTACCEN ABU:
Kada tsananin jinya ko jinkirin waraka yarudi maras lafiya har yakaishi yin magani da harataccen abu domin yin hakan ya sabawa hankali da kuma nassin shari’a,
A bangaren hankali hakika an haramta haramne ko kiyaye lafiyar mutum da mutuncinsa da ma rayuwarsa,
A bangaren NASSI kuma=
= ANNABI SAW yace “ba’a samun abinda yake wajen ALLAH SW sai ta hanyar biyayya ga ALLAH” {ALHKM, IBN-HIBBAN, ASSAHEEHA-3866}
= ANNABI SAW yace “ALLAH ya halicci cuta da magani kunemi magani amma kada kuyi magani da haramun” {ASSAHEEHA-1633}
=ANNABI SAW yace “ALLAH bai sanya muku warakarku cikin abinda ya haramta muku ba” {BHR, TDABRANY}

(2) ZAGIN CUTA/JINYA:
Bai halatta ga maras lafiya yazagi cutarda yake damunsa ba ko yatsine mata ba, kamar yace- zazzabi ko hawan jini ko ibola- yace mummunar ciwone! Ko yace ALLAH yatsine mata! hakan bai halattaba saboda dalilai kamar haka=
= ANNABI SAW yaje gidan UMMUS SA’IB sai yatarar tana karkarwa?
Sai yace “me yasameki?”
Sai tace- zazzabine kuma kada ALLAH yayi masa albarka!
Sai ANNABI SAW yace “kada kizagi zazzabi domin yana tafiyarda zunubbai kamar yadda wutar makeri take tafiyarda dottin karfe” {MSLM}
=ANNABI SAW ya kasance aduk lokacinda yazo gaida maras lafiya sai yace “kada kadamu- tsarkine insha’allahu” {BHR}
Kaga yabawa jinyar yayi,

(3) ZUWA WURIN BOKAYE:
= ANNABI SAW yace “duk wanda yaje wurin boka yatambayeshi abu baza’a karbi sallansa na kwanaki 40 ba” {MSLM} wannan mafa in bai gaskanta bokan ba, in ya gaskantafa?
=ANNABI SAW yace “duk wanda yaje wurin mai duba ko mai sihiri ko boka kuma yagaskantashi hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa ANNABI SAW” {ABU-YA’ALA, BAZZAAR, TDABRANY}

(4) YAYE AL’AURA:
Bai halatta ga maras lafiya yabar tsiraicinsa a waje ba, ya suturta ko a suturta masa,
=ALLAH yace <<ya ku ‘yan Adam hakika mun saukar muku tufafinda zai lullube muku tsiraicinku>> [SRT A’ARAF-26]
= ANNABI SAW yace “kada na miji yakalli tsiraicin dan’uwansa hakama mace” {MSLM}

(5) ADU’R FANSAR ALLAH AKANSA:
=ANNABI SAW yazo gaida wani maras lafiya sai yaga ya rame ya kanjame ya lalace,
Sai yace dashi “shin kana adu’a kuwa?
Sai yace- E, ina adu’a ina cewa- YA ALLAH! azabar laifukana da zakayi mini a lahira kayi mini madadinsa a lahira!
Sai ANNABI SAW yace ” SUBHANALLAH! bazaka iyaba, donme bazakace
اللهم آتنا في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة وقنا عذاب النار
Sai mutumin yafara wannan adu’ar sai ya warke, {MSLM}

(6) BURIN MUTUWA:
= ANNABI SAW yace “kada dayanku yayi burin mutuwa don cutarda yasameshi- domin in shi mai kirkine maiyiwuwa yakara, in kuma mai sabone mai yiwuwa yatuba”

(7) SAKACIN IBADA:
Bai halatta maras lafiya yalangabe yaki ibada ba, madadin hakama yazage dantse da ibada don samun karin guzuri,
=ALLAH yace <<kabautawa ubangijinka har mutuwa yazo maka>> [SRT
= ALLAH yace <<ma’abota hankula- wadanda suke ambaton ALLAH a tsaye da zaune da kuma a kwance>> [SRT ALI-IMRANA]
= Yayinda ANNABI SAW yayi rashin lafiyar ajali daf da rasuwarsa akwai ranarda yayi yunkurin fita masallaci in yayi yunkuri sai yasuma in ya farfado sai yasake yunkuri, har sau 7 yana suma, {SAHIH BUHARI}
= SHEIKH USMAN IBN FODIO yana jinya yayi yunkurin hawa doki don yafita da’awa haka yacika a wannan halin, {INFAQUL MAISUR FI TARIKHI BILADIT TUKRUR}
= Dayanku yana aikata kyawawan aiki saura kiris yamutu yashiga aljanna sai yasauya zuwa miyagun ayyuka sai yamutu yashiga wuta”
Don haka kada kayi sakacin ibada a rashin lafiya kuma kaguji boka don kaucewa mutuwa akan kafirci

(8) SAKACI DA NAJASA DA TSARKI:
Kaguji zama a najasar bawali da bayan gida musammanma lokacinda kake jinya, hakama ya dace ga masu jiyyar maras lafiya su tsarkakeshi daga najasa akoda yaushe don ba’asan yaushe mutuwa zaizo masaba!
= ALLAH yace <<lalle ALLAH yanason masu tuba kuma yanason masu tsarki>> [SRT BQR]
kishiyar maganar shine ALLAH bayason masu najasa,
= kuma ANNABI SAW ya tarada kaburbura biyu ana azabtar da wadanda suke cikinta Sai yace “dayan baya tsarkaka daga bawali”
= ANNABI SAW yace “Ku tsarkaka daga bawali domin dukkan azaban kabari daga bawaline”

(9) YANKE TSAMMANI:
Bai dace maras lafiya ya yanke tsammani daga samun sauki da waraka ba,
= ANNABI YUSUF A/S ya bata sama da shekaru 30 amma babansa ANNABI YAQUB A/S yake cewa sauran ‘ya’yansa <<ya ku ‘ya’yana kutafi kunemo YUSUF da dan’uwansa kada kuyanke tsammani daga rahamar ALLAH, domin babu mai yanke tsammani daga rahamar ALLAH sai kafirai>> [SRT YUSUF]
= ANNABI AYUBA A/S yayi fama da jinya Samara shekaru 10, amma daga baya ALLAH yabashi lafiya yamayar masa da arzikinsa da iyalansa sama da da, [SRT ANBIYA’I]

(10) RASHIN ADU’A:
Bai dace maras lafiya yakauracewa adu’ar samun lafiyaba, domin ANNABI AYUBA ya nace da adu’ane shiyasa ALLAH yabashi lafiya,
=ALLAH yace <<AYUBA ya roki ubangijinsa yace YA UBANGIJI cuta ya shafeni kuma kaine majinkan masu jinkai>> [SRT ANBIYA’I]

***** KASHI NA-2 *****
RUFEWA:
Zan rufe da Hadisan ANNABI SAW guda 2=
i- ANNABI SAW yace “kabautawa ALLAH lokacinda kake cikin yalwa zai tuna dakai lokacinda kake cikin tsanani”
ii- ANNABI SAW yace “karibaci lafiyarka tun kafin rashin lafiyarka”

YA ALLAH KABAMU JURIYA DA TSABATI A LAFIYA DA RASHIN LAFIYA.
Amiiiiiiiiiiin.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website