Musulinci taskar rayuwa : Tsafta ga namiji da mace//1

TSAFTA GA NAMIJI DA MACE //1

Rayuwar Manzon Allah (SAW) shine mafi kyawun rayuwa, kuma ya koyar da musulmai dukkanin kyawawan dabi’u. Tsarki da tsafta suna da babban matsayi a addinin musulunci, wannan ne ma har yasa Annabi (SAW) yace:

ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ‏<< ﺍﻟﻄُّﻬُﻮﺭُ ﺷَﻄْﺮُ ﺍﻹِﻳﻤَﺎﻥِ>>

“Tsafta tana daga cikin imani”.

Yana da kyau ko wane musulmi mace ko namiji su fahimci muhimmancin tsafta Kuma su rinka kasancewa cikin sa a koda yaushe. Nuna halin ko in kula yana jawo ma mutum cututtuka da rashin girma a wurin mutane, kuma zai sa mutane su yi nesa nesa da mutum saboda kada yazo kusa dasu su ji wani wari ko tsami na fitowa daga jikin sa. Zan tattaunawa Abubuwan tsafta da yanda za’ayi tsafta din dama shawarwari Idan mutum yana da kasala wurin wasu tsafta.

Farko zan fara ne da rage gashin wurare biyu na jikin mutum, wato hammata da kuma kasan sa, kamar yanda yazo a hadisi Abu Hurairah yaji Annabi (SAW) yana cewa:

عن ابي هريرة رضي الله عنه قال ،سمعت رسول الله صلي الله عليه وسلم يقول”الفطرة خمس الختان، والااستحداد، وقص الشارب، وتقليم الاظفار،وتنف الا ابط”.

“Ayyukan da’a guda 5 ne: “Kaciya, da cire gashin hammata, da rage gashin baki, da yanke farce, da tsige (cire) gashin mara”.[Bukhari].

HAMMATA DA KASAN MUTUM:
Wainnan wuraren biyu suna da mutukar bukatar kulawa, saboda wurare ne da basu da wuyan sun fara fitar da wari, domin su kullum a lullube suke. Don haka ne Manzon Allah (SAW) Ya umurci mutane da rage gashin wurin duk bayan 40 days. Sannan ba dole sai 40days ba saboda akwai masu kufan gashi da kafin ma 40days gashi ya fito musu sosai.

ABUBUWAN DA AKE AMFANI DASU WURIN SHAVING 👇🏽

Ko wanne mutum akwai abin da yake amfani dashi wurin cire gashi, sai dai wasu abin da suke amfani dashi yana da hatsari sosai, misalin masu amfani da razor (reza) ina shawartan maza da mata dasu dai na sa razor saboda mutum zai iya ji ma kansa mummunan rauni.

Abin da za’a nema sune:
1.Shaving cream/Shaving powder
2.Shaving razor Stick
3.Zaitun.

1.Shaving cream dai kala kala ne, sai wanda mutum ya zaba, amma wanda naga mutane suka fi sani ko suka fi amfani dashi shine VEET. Ina jin kamar 600 ake siyar dashi, idan mutum ya je toilet zayyi shaving sai ya shafa shi wannan cream din a in da gashi suka fito masa, sannan sai ya bashi kamar 5mnt haka, Akwai abun da yake zuwa a ciki na roba, dashi zaki fara cire mai da gashi kafin ki wanke, mutum zai ga dukkanin gashin ya fita sumul. Shaving cream amfanin sa na da yawa, bayan cire maka gashi da zayyi, still zai sa gashi ya jima bai fito maka a wurin ba, ba kamar kayi amfani da shaving stick ba. Sannan shaving cream bayi da wari kamar yanda naji wasu mata nata surutai a kai, wata ma kila bata taba amfani dashi ba labari taji Kawai. Don haka bayi da wari kamar yanda ake fadi.

2.Shaving Power, shima din kala kala ne, amma yawanci maza sun fi amfani da shaving powder, amma shi gaskiya yana da wari sosai, shiyasa mutane ke gudunsa, kuma yana da karfi sosai da sosai, saboda shi idan ya dade a jikin mutum zai iya farfasa ma mutum fata, yanda yake, fari ne kamar powder, idan zaki yi amfani dashi sai ki debi dai dai yanda zai isheki ki dan sa masa ruwa sannan a shafa.

3.Shaving razor stick: Ga mace ana so ta kiyaye sa wannan cream din ko powder a dai dai wurin Farjinta, saboda guje ma cutar wa, a sama zaki sa, kasan kuma sai kiyi amfani da Shaving stick ki cire ragowar. Sannan shi shaving stick ana ajiye shine saboda randa baka jin sa cream sai amutum yayi amfani da stick din. Kuma is safer akan kiyi amfani da da reza.

4. Zaitun, mutane dayawa idan sun yi shaving haka suke barin wurin, to ba a haka, duk lokacin da mutum yayi shaving ya wanke wurin, kafin ya fito ko bayan ya fito toilet sai ya shafa zaitun sosai a wuraren nan guda biyu, tabbas mutum zai sami jin dadi a jikin sa ma, musamman mace.

Gaskiya kazanta ya kai kazanta ace namiji ko mace basa rage gashin jikin su, saboda Al’aura wuri ne da yake fitar da abubuwa dayawa musamman ga mace, idan kika ce ba zaki tsafta ce wurin ki gyara shi ba, to dukkan kazantar da kika fitar shi ma zai nemi wuri ne ya zauna, duk wannan jinin zai makale ke kin dauka kin wanke amma kuma ya nemi wuri a cikin gashin ya makale, sannan ba za’a raba ki da kuraje da soshe soshe ba tun da dai kin bar wurin ba tsafta. Sannan babu aji ga mace ko namiji su daga hammata aga gashi dunguzun duk datti, don haka yana da kyau a rinka yanke gashi a kai a kai.

  • 🌿Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website