Musulinci taskar rayuwa – Tsafta tsakanin namiji da mace//2


TSAFTA TSAKANIN NAMIJI DA MACE //2
DEODORANT

Idan muka gama da zancen yanke gashin hammata da na kasa, yana da kyau mutane su san amfanin deodorant (turaren hammata), domin yana da mutukar muhimmanci a hammata, abun ba dadi ace ka shiga jama’a hammatar ka na cutar da mutane saboda wari, Akwai wainda basu da irin wannan warin, amma wani sai yana yi yana tsaftace kansa da abubuwan kamshi sosai, kuma shi deodorant zan iya cewa yafi turare amfani a jikin mutum, saboda koda mutum yayi kwalliya yasa turare still zaka iya jin warin hammatar sa, saboda shi hammatar ba a sa masa nasa turaren ba.

Deodorant shima kala kala ne, akwai me maiko, akwai na fesawa, akwai kuma wanda kamar vaseline yake ji. Sai ka duba kaga shin wanne ne zai dace dani, idan kai mai yawan ruwan hammata ne, to akwai na fesawa mai qamar da hammata 24hrs, shi ya dace mutum ya siya, sannan mutum ya kiyaye siyan fake, wainda ba daga company suke ba, ko mutum yayi amfani dasu zai ga sai dai su kara masa wari ma, kuma akwai kamfanoni wainda suke yin marasa kyau, don haka ni dai wainnan 3 din na yarda dasu. Akwai Rexona, Nivea Da kuma Dove. Suna da kyau sosai kuma mutane dayawa sun yarda da mayukan su na hammata.

Sannan akwai deodorant body spray, su kuma wainnan turaren jiki ne amma ana shafa su a hammata kuma suna kamar da zufa tare da bada kamshi mai dadi. Mace zata iya neman su Explore, Eskoda (pink) da touch me (nabeel) koma wasu su dai-dai karfin mutum, suna da kyau sosai.

Sannan ga mace, ana so ki na sa wa kasan ki Musk fari ko ja, yana sa wurin kamshi, sai wanke wurin da soap na Habbatus Sauda ko Zaitun, ana samun su a Islamic chemist.

Kada ki rinka cutar da mijin ki, kina kin tsaftace jikin ki, a kula. Haka nan kai ma saboda tsafta da kwalliya yana da mutukar muhimmanci ga dan adam.

  • Yar’uwar ku Sadeeya Lawal Abubakar

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website