Yara manyan gobe – 3

Yara manyan gobe 3

Assalamu alaikum barkarmu da sake saduwa a wannan gida namu mai tarin albarka Fitila24, a kuma wannan shirinamu shirin Yara Manyan Gobe. Da fatan muna lafiya.

A shirinmu daya gabata mun tsayane a dai-dai inda zamu fara bayani akan gudunmawar iyaye wajan inganta tarbiyyar yara, da yardar Allah zamu dora daga inda muka tsaya.

GUDUNMAWAR IYAYE WAJAN TARBIYAR YARA

Hakika da bukatar iyaye su san cewa, sune matakin farko wajan tabbatar da an inganta tarbiya.

Kuma su sani hakkine babba a kansu, sannan aikine bana wasaba.

Kuma su sani wannan aiki yana farawane tun kafin aure,

A matsayinka na mahaifi kabbatar dacewa Kasamu nagartacciyar Mata mai tarbiya, domin babu yadda za’ayi mutum ya bada abinda bashi dashi, idan bata kasance me tarbiyaba, to hakika yaranka sun rasa wani babban sashi na ingantuwar tarbiyarsu.

Sannan kema a matsayinki ta mahaifiya dole ki natsu, ki tabbatar wanda zaki zaba a matsayin uba ga yaranki, ya kasance nagartacce, masanin addini da rayuwa, domin tabbatar indantuwan tarbiyar yaranki tana da alaka da halin mahaifinsu.

Tunda wannan shiri na yarane, bazamu tswaita bayani akan hanyar samun miji na gari ko mata ta gariba, sabida a wannan gida akwai shiri na musamman wanda aka tanada domin ma’aurata mai suna GIDAN AURE, gamai bukatar yalwataccan bayani akan rayuwar ma’aurata kafin aure ko bayan aure, yana iya ziyartar wannan shiri, sai dai mun tabone iya bokata.

Bayan wannan, toh yanzu munji dai hakkin yaranmu a kanmu kafin aure, kuma shine mataki na farko wajan tabbatar ingantar tarbiyar YARA.

Sannan sai mu shigo daga ciki, ma’ana bayan anyi auran,

Hakika addininmu (Musulunci) ya shiryar damu wasu abubuwa dan tsarkake kawunanmu da iyalinmu,

Daga ciki akwai cin halal, cin halal wani al’amarini babba, wanda rashin cin halal zai iya haifar mana da samun mummunan zuri’a. Domin jikinmu yana ginuwane daga abinda mukeci, toh idan bamu tabbatar da mun tsaftace hanyar cinmuba, gangar jikinmu zata sama mana sinadaran haihuwarmu daga abinda mukaci na haram, kaga tun daganan an samu matsalar tarbiya. Abin da za’a haifa zai iya zama mara kirki, Allah ya kyauta. Kuma akwai addu’a da Manzan Rahama ya koyamana yayin kwanciyar aure, rashin yinta yana taimakawa wajan lalacewar tarbiyar yaranmu,

Da addu’ar “Allahumma jannibnash shai’dan, wa jannibnashi shai’dana mimma razak’attana”

Fassara “Allah ka karemu daga shidan, kuma ka kare shidan daga abinda zaka azurtamu dashi”.
Allah ya mana jagora

Daganan sai mu tsallaka zuga lokacin da yaro yake ciki,

Wadanne abubuwane Yara ke bukata dan inganta tarbiya, lokacin da suke ciki?

‘Yan’uwa yan albarka, zamu dasa aya anan sai mako mai zuwa Insha Allah zamu cigaba daga inda muka tsaya.

Ku tara a mako mai zuwa, dan cigaban wannan shiri. Inda zamu ji jerin rukunnan al’ummar dake samar da tarbiya ga yara, da kuma gudunmawar da kowane bangaren rukunin, wajan ingantar tarbiyar ko gurbatarta, kai tsaye a cikin wannan shiri.

Rana shiri:- Asabar
Tare da Ni :- Zainab S Adam

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website