takaddama_da_hanyoyin_sasantawa

TAKADAMA DA HANYOYIN SASANTAWA – FITOWA TA 1: BAYANAI

FITOWA NA 1: BAYANAI

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halici dan Adam daga babu kuma ya sanya masa dabara, hankali da hikima. Tsira da aminci su tabbata ga manzon Allah (S.A.W).

Wannan shirin na Takaddama da Hanyoyi Sasantawa zai dinga zuwa muku a kowani Ranakun Talata da Juma’a in sha Allah, inda muke sa ran haska muka menene Takaddama, Bayananta, Canje-canje ta, Makamashin ta, Ire-iren ta, Abubuwan da suke haddasa ta, da sauran su har zuwa yarda ake magance takaddama in sha Allah. Ku biyo mu

MAKASUDAN BAYANAI GAME DA TAKADDAMA

Bayyanar Takaddama a duniya: Takaddama al’amari ne gama garin wanda yake aukuwa tsakanin mutum da waninsa, ko kungiyoyi da al’ummomi na duniya baki dayanta. Saboda haka bai tsaya kawai a wuraren da mu ke ba. Daga shekara 1989 zuwa yanzu akan samu aukuwar yake-yake kimanin guda 30 zuwa 34 a kowace shekara a duniya. Yawacin wadannan rikice – rikice suna aukuwa ne kasashe masu tasowa na duniya musamman na Afrika.

Bayyanar Takaddama a Nigeriya: Babban rikicin da aka yi a Nigeria shi ne yakin basasa na Biyafara. Bayan shi, an yi kananan rikice – rikice har fiye da 40 a sassa daban – daban na kasar nan.

Illolin Takaddama: Illolin irin wadannan takaddama sun hada da Asarar rayuka, dukiyoyi, lokaci, rashin muhalli ko matsuguni, firgici, bakin ciki, fushi, rashi yarda, talauci, da koma bayan al’amura ko rashin ci gaba.

 

Darasin da za mu koya daga sabon salon yaki na zamani shine: “zaman lafiya komai tsadar sa yafi yaki komai arhansa”. Misali, ana kasha makuda kudi har kimanin dala miliyan 80 son samar da jirgin yaki wato (F. 16 Jet Fighter) wanda kuma abokan gaba suna iya tarwatsa shi cikin dan lokaci kadan da makami mai linzami (missle). Wannan kudi ya fi karfin yawan kudaden kasafin kudin kasashen Afrika 10 da suke aiwatarwa a duk shekara wato (budget) idan aka tara su gaba daya. Wannan ya nuna a fili cewa lallai yaki yana tsotse dukiyoyi da albarkatun kasa da za a iya amfani das u don magance fatara da bunkasar ilimi da sha’anin kiwon lafiya

 

A tsakanin shekarun 1945 da 1989, an samu afkuwar mace mace ta sanadiyyar yaki kwatankwacin miliyan 30 a duniya sannan kuma kimanin mutane miliyan 17 sun rasa gidajensu ban da wandanda suka yi gudun hijira zuwa wasu wurare don neman mafaka

Sai kuma idan Allah ya Kaimu Ranar Talata mai zuwa (26/04/2016) sai mu shigaba

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website