TAKADDAMA DA HANYOYIN SASSANTAWA FITOWA NA 7: SALON SARRAFA TAKADDAMA

Mataki na Farko
Akan shiga halin takaddama ne idan bukatu ko damuwar mutum biyu ko fiye da haka suka babanta kuma suka kasa daidaituwa. Domin tantance hanyoyin da mutane suke bi wajen SARRAFA takaddama ana iya fayyace halayen mutane ta wadannan hanyoyin.

Nuna Son Mai
Wannan yana nuna irin kokarin  da mutum kan yi domin ganin biyan bukatar sa da damuwarsa.

Bada Hadinkai
Wannan shine yake nuna irin iyakacin da mutum yake yi wajen biyan bukatunsa da abin da Ya dame shi tare da biyan bukatunsa wadansu mutane. Ana iya amfani da wadannan muhimmanci hanyoyin biyu na sakin halayen mutane (kamar yadda bayani ya gabata) wajen faddada matakan sarrafa takaddama guda biyar. Su ne: Mallaka, Gasa, Kau da kai, Hadin gwiwa, Sassaucin ra’ayi.

Danniya da Gasa
Mutum mai danniya da son gasa yakan zamo mai son kansa sannan kuma ya yi ta kokarin biyan bukatun kansa da gumin wasu. Wannan tarbiya ce ta nuna iko. Kuma matsayi ne mai nuna cewa “dole ne mutum ya samu nasara”. Kuma ya nuna dole ne mutum ya tashi tsaye don neman yancin kansa. Wannan ya kunshi kare wani matsayi ta hanyar muhawara ko ta nuna mukami ko dukiya. Wato a kullum mutum yana son wasu su sami rashin nasara.

Saukin kai
A nan mutum ba ya nuna son kansa kuma yakan zamo mai bada hadin kai ne, sabanin mai son yin gasa. Idan kana da saukin kai kakan sadaukar da bukatunka domin biyan bukatun wasu. Ana iya samun kyakkyawan biyan bukata ta wannan salon.

Kau da kai ko Gujewa
Mai irin wannan hali ba ya nuna son zuciya amma kuma ba ya ba sauran mutane hadin kai. Ba ya damuwa da neman biyan bukatansa ko na wasu mutane. A nan mutum ba ya tsayawa ya warware matsala da ke gabansa. Watakila yin hakan takan zamanto wata hanya ce ta lalama wajen sarrafa takaddama don yin jinkiri zuwa wani lokaci da Ya fi dacewa domin warware wannan matsalar. Kuma yana iya kaurace wa takaddama gaba dayanta Wanda hakan zai iya kaiwa ga tabarbarewar dangantaka.

Shawo ka Takaddama ta Hadin Gwiwa
Wannan shi ne kasancewar mutum mai son ya biya bukatun kansa da kuma bada hadin kai. Wannan ya saba da salon kau da kai daga barin takaddama. Mutumin da ke da irin wannan hali yakan yi aiki tare da wasu mutane domin neman wata matsala da zai gamsar da bukatun duka. Wannan yana nufin tattaunawa, kyakkyawan saurare kuma yana nufin fahimtar bukatu da damuwar mutum kansa da wa’inda tare da fitar da matsala akan wadannan damuwa don kaiwa ga nasara. A nan duka bangarorin biyu sukan yi nasara.

warware Matsala
Wannan shi ne yin sassauci wajen neman son biyan bukatun kai da kuma sassauci wajen hada kai da wasu domin biyan bukatunsu ko damuwar su. Idan mutum ya yi sassauci yana neman wata matsala ce wacce za ta samu karbuwa da gamsuwa da dukkannin bangarori idan mutum ya yi sassauci.

image
takaddama_da_hanyoyin_sasantawa

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments