TAKADDAMA DA HANYOYIN SASSANTAWA FITOWA NA 8: SALON SARRAFA TAKADDAMA II

Mataki na Biyu (2)

Duk da yake kowa yana da hanyar da yake bi wajen warware takaddama, ana iya kasa hanyoyin zuwa kashi uku kamar haka.

  • Gujewa takaddama
  • Fito na fito ko fada
  • Warware matsala

Gujewa

Wannan hanya ita ce aka fi yawan bi wajen sarrafa takaddama. Muna iya yanke shawarar mu kauce wa takaddama da ta hada mu da wani mutum, mu kauda kai mu nuna rashin damuwarmu a zahiri, kamar babu abin da ya taba faruwa koda yake abin ya yi mana zafi ya bata mana rai. Ya kamata mu lura da cewa irin wannan hanyar sarrafa takaddama yawancin lokacin takan bar mu cikin matukar jin zafi da bacin rai ko fushi.

Irin wannan salo ana iya kwatanta shi da matar auren da take share datti ta tattara shi a karkashin shimfida ko dardumar dakinta; babu makawa wata rana dattin zai yi yawa har ya fito fili. Irin wannan hanya ko salo yana bada samun nasara ko rashin nasara, don haka irin wannan matsala aba ce wadda mutum yana iya samun biyan bukatar shi kuma waninsa bai samu komai ba na bukatansa. Wannan ba Ya warware matsala sai dai ya jinkirta matsala zuwa wani dan lokaci (an kashe maciji ba a safe kanshi ba)

Amma duk da haka akan samu wasu yanayin inda wannan salo ke da amfani. Misali, gujewa takaddama yana bada damar samun lokacin da za a tsaya a yi tunani a kan matakin da za a iya bi nan gaba.

Fito na fito ko fada

Wadansu mutane sukan yi jayyaya da wadanda suke takaddama da su. Wadansu kuma sukan yi dammara su kalubalanci mutanen da wata husama ta hada su da su. Sukan yi barazana ko su kai bugu ko hauri ko su yi hargowa da cin mutunci kuma sukan dage akan ra’ayinsu su ki yarda da ra’ayin waninsu. Irin wannan hanya ko salo yakan kai barkewar rikici ko rashin hankali.

Yin amfani da irin wannan dama ba safai ba ne yakan kawo biyan bukata ko nasara ga dukkan mutanen da ke rikici. A wasu halaye ko yanayin kuma yin fito na fito yakan sa Wanda Ya fi karfi Ya sami nasara yayin da Mai rauni zai yi hasara.

Warware Matsala ta Hadin Gwiwa

Wannan ita ce hanya wacce abokan hamayya ko adawa ko takaddama ke amfani da ita wajen sauraro da nufin gano ainihin musabbabin takaddama don magance matsalolin. Mutanen da suke amfani da wannan salo idan suna takaddama da junansu mutane ne wadanda suka san muhimmancin girmama bambancin da ke tsakanin su tare da kokarin neman hanyoyin da za a warware matsalar.

Kuma bugu da Kari, mutanan da suke amfani da wannan hanya ba su damuwa da wane ne yake da gaskiya ko kuma wane ne bashi da gaskiya. Sukan dauki takaddama aba ce wadda ke bukatar hadin kai da kuma domin warware ta. Wannan hanya tana bayar da damar samun gamsuwa ga kowane bangare. Wannan yanayin yana sa kowane sashi gamsuwa saboda samun biyan bukatun su da kuma ganin dangantakarsu ta sake farfadowa.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments