Taskar So – 7

Taskar So 7

Assalamu alaikum Masoya ‘yan-albarka, masu jimirin kasancewa damu a wannan gida Fitila24, a kuma wannan shiri mai farin jini da tarin masoya wato Taskar So.

Shiri mai bayani akan So da Soyayya da Kauna, da daukacin abinda ya shafesu.

Yau gashi Allah ya kawomu cikin wannan gida Fitila24 dan cigaban wannan shiri Taskar So, inda zamu dora daga inda muka tsaya wancan mako.

Ga masu bibiyar wannan shiri idan bamu mantaba, mun tsayane a dai-dai inda zamu bayyana wasu sirrika masu matukar mahimmanci a rayuwar masoya,

Wadannan sirrika kuwa sune:-

Yadda mace zata gane masoyi na gaskiya, mai fatan kasancewa da ita a rayuwa ta da’iman (rayuwar aure)
Da kuma
Yadda namiji zai gane masoyiya ta gaskiya mai fatan kasancewa dashi a matsayin uban ‘ya’yanta.

Kamar dai yadda muka sani, duniya da fadi kuma abubuwa suna da yawa, sannan ga shi mutane nau’i-nau’i,

Amma duk da haka zamu kawo wadansu abubuwa da zasu taimaka matuk’a wajan gano amsar wadancan tambayoyi.

Yadda zaka gane tana SOn-ka so na gaskiya, ba yaudarata take yi maka ba:-

 1. 1- Zata rika girmamaka da girmama ra’ayinka.
  2- Zata girmama iyayanka kuma zata mutuntasu,
  3- Zata rika shigar dakai cikin ‘yan’uwanta tana baiyanaka a matsayin masoyinta
  4- Zata girmama abokanka kuma zata mutuntasu
  5- Zata rika bawa kawayanta labarinka, tana baiyanaka a matsayin masoyinta
  6- Zata so abinda kake so
  7- Zata k’i abinda kake k’i
  8- Zatai farin ciki, da farin cikin ka
  9- Zata damu da damuwarka
  11- Zata rika baka uziri akan kurakuranka
  12- Zata rika yafemaka laifukanka a gareta
  13- Zata rika iyayinta wajan ganin ta faranta maka, da furucinta da kwalliyarta
  14- Zata rika boye aibinka
  15- Bazata taba bari a batakaba agabanta. DS

Yadda zaki gane yana sanki so na gaskiya ba yaudaraba:-

Shima dai duk alamomin dayane da wadancan alamu sai dai dan karin da baza’a rasaba kamar:-

1- Kokarin shiga cikin ‘yan’uwanki, in bada gaske ya-ke-yi ba ba ze bari su sanshiba
2- Kokarin gabatar da kyauta a gareki, daidai karfinsa
3- San kasancewa dake ta ahnyar zuwa gidanku, in kuma hakan baisamu sabida nisa ko wani dalili, toh ta hanyar kira ta waya, DS. ‘Yar’uwa zaki bibiyi wadancan alamomi da aka lissafa na yadda zai gane ki na sanshi, sannan ki hada da wadannan. Zasu taimaka miki wajan gane cewa yana sankine da aure.
Mun yi isharane garesu sabida takaitawa.

Sannan alamomin da ake samunsu a dukkan bangaren in da soyayya ta gaskiya:-

-Amana
-Gaskiya
da dai sauransu

‘Yan’uwa yan albarka zamu ja linzamun shirinmu anan sai Allah ya kaimu mako mai zuwa, inada zamu zo muku da wani saban shiri.

Amma kafinnan zamu saurari Abu~Sajida da kalaman So

Kalaman bakin Abu~Sajida

* Kinzam bugun zuciyaata, tunaninki ya mamayeta
* Kinzamto sashin jikiina, sarauniyar zuciyata
* Dake nake takama a rayuwata, in babu ke ni bansan yadda zan yiba….

‘Yan’uwa sai Allah ya kaimu
Naku a Kullum mai fatan farin cikinku:- H.Y (Abu~Sajida)

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website