Yara manyan gobr 4. – Tarbiyar ciki (juna biyu)

Yara manyan gobe 4

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu,

‘Yan’uwa barkarmu da sake saduwa a wannan gida mai albarka (Fitla24), a kuma wannan shiri na musamman (Yara manyan gobe). Shirin dake fayyacewa dangane da kula da tarbiyar yaranmu, matakan tarbiya, da masu tarbiyar da sauran al’amuran dake da alak’a da tarbiyar yara.

A makon daya gabata mun tsayane a inda zamu fara bayani game da abubuwan da yara ke bukata yayin da suke ciki, dan inganta tarbiyarsu, cikin amincewar Ubangiji gashi mun dawo dan cigaba daga inda muga shaya….

Wadanne abubuwane Yara ke bukata dan inganta tarbiyarsu, lokacin da suke ciki?

Hakika akwai wasu abubuwa da ake bukatar iyaye su kula dasu yayin da uwar gida ta samu cikin (juna biyu) dan inganta tarbiyar abinda ke cikin, bangaran ruhinsa da ganganjikinsa.

A matsayinka na me-gida, ana bukatar ka kula, ka tabbatar da tana cin abincin halal, sannan me gina jiki, domin hakan ze taimakawa yaran wajan kara masa lafiya, da haska zuciyarsa, sabida cin halal yana kusantar da bawa zuwa ga Ubangijinsa.

Sannan ka mu’amalanceta da tausayawa, ka tsare mata jinta da ganinta, dan hakan yana da tasiri ga abinda take dauke dashi (yaran), kasancewarta cikin tashin hankali, ze hana yaran ya samu sukunin zama, kuma hakan ze iya tasiri a gareshi bayan haihuwarsa, ya kasance in bai ji wannan hayaniyarba toh fah ba ze ji dadiba, sabi da ya saba tun yana ciki.

Ke kuma mahaifiya kema dolene ki kula wajan cin abu me kyau, domin in bakya cin me kyau na jikinki ze yi amfani dashi, kuma ba zaki samu kuzarin motsa jikiba,
Ana bukatarki da ki sance kina kokari wajan motsa jiki, hakan ze taimaka masa a lafiyarsa, da gabobonsa.
Sannan ki rage jin zantukan da basu daceba, sauraran wakewake, ko zage-zake, ko makamantansu.
Ki lizimci sauraran zantukan alheri, karatun Alkur’ani, da wa’azozi, da dai sauran al’amuran alheri, ban garan ji kenan.
Sannan bangaran harshi (ki kiyaye furta kalaman da basu daceba, ashariya da yin wakokin batsa, ko makamantansu, ki danyatar da harshanki da yawan zikiri da karatun Al’kur’ani, hakan wata hanyace ta isar da wadannan tarbiya ga abinda ke cikin (yaran).
Kuma ki kiyayewa idanonki kallan abubuwan da basu daceba, kallan haram, da munanan abubuwa, da abin da ganinsa ze tashi hankalinki.

Sannan gabadayanku (iyaye) zaku dage wajan yin addu’ar shiriya ga abinda Allah ze auzrtaku da shi, tun kafin zuwanshi duniya.

‘Yan’uwa zamu dakata anan sai Allah ya kaimu mako me zuwa, mu tara dan cigaba daga inda muka tsaya.

Tare da ni:- Zainab S Adam.

Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan FITILA24!

Ga mai bukatar samun shirye-shiryan FITILA24 a shafin Whatsapp sai ya biyomu ta wannan link din

ko a biyomu a shafinmuna.

Fb Page: - Facebook Page Fb Group: - Fitila24 Twitter: - @Fitila24 .

Comments

comments

Leave a Reply

Name *
Email *
Website